Mutanen Atiku Sun Koma APC, za Su Samawa Tinubu Kuri'a Miliyan 10
- Wata ƙungiyar wayar da kan matasa da ke da alaƙa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ta sanar da cewa ta koma APC
- A ranar Alhamis ta ce tana goyon bayan sake zaɓen shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027, tare da alƙawarin samar masa da ƙuri’u miliyan 10
- Ta bayyana hakan ne a wajen bikin ƙaddamar da ita wanda kuma a nan fadi tsarinta na wayar da kan jama’a tare tabbatar da haɗuwarta da City Boy
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wata ƙungiyar siyasa mai wayar da kan matasa da ta ce tana da alaƙa da Atiku Abubakar ta goyi bayan sake zaɓen shugaba Bola Tinubu tare da yin alƙawarin tattara masa ƙuri’u miliyan 10 a zaben 2027.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Matashin da ya kirkiri muryar Tinubu ta bogi ya shiga komar ƴan sanda
Ƙungiyar ta sanar da goyon bayan ne a Abuja ranar Alhamis a wajen ƙaddamar da The Bridge for Renewed Hope a matakin ƙasa, wani dandalin wayar da kan jama’a kan harkokin siyasa.

Source: Facebook
A wani sako da kungiyar City Boy ta wallafa a shafinta na X, ta ce kungiyar magoya bayan Atikun ta hade da ita domin tabbatar a nasarar Bola Tinubu a 2027.
Kungiyar Atiku ta koma APC
Jagoran kungiyar, Rowland Odih ya ce mambobi da dama, waɗanda a baya suke da alaƙa da tsarin siyasar Atiku, sun yanke shawarar goyon bayan Tinubu aiki tare da matasa da ya ke yi.
Odih ya ce ƙungiyar za ta yi aiki domin ƙara shigar da matasa cikin harkokin mulki tare da tattara jama'a su goyi bayan Tinubu gabanin zaɓen 2027.
“Za mu yi aiki dare da rana domin tabbatar da cewa mun samar wa shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u miliyan 10 a shekarar 2027,”
In ji shi.
Dalilin goyon bayan Tinubu
Shugabannin kungiyar sun bayyana cewa sun shafe shekaru da dama suna goyon bayan Atiku Abubakar, amma yanzu sun gano cewa tafiyar Bola Tinubu ce mai dorewa.

Kara karanta wannan
Bayan sukar kalamansa a 2023, Peter Obi ya shawarci matasa kan siyasar addini, kabilanci
The Cable ta rahoto sun ce:
“Kimanin shekaru 20 da suka gabata, mun fara ne da tsarin matasan Atiku, amma a yau muna cikin wata sabuwar alkibla saboda mun ga shugabanci mai aiwatar da aiki.
“Yanzu mun ga gwamnatin da ke damawa da matasa. Sama da kashi 60% na naɗe-naɗen da muke gani matasa ne ke cin gajiyarsu. Duk da cewa wasu daga cikin waɗannan manufofi suna da raɗaɗi, sun shimfiɗa tushen ci gaba mai dorewa.”

Source: Facebook
Odih ya ce ayyukan more rayuwa da ake aiwatarwa a faɗin ƙasar suna nuna manufar da gwamnatin Bola Tinubu ke da shi wajen ci gaban kasa.
Za a nuna ayyukan Tinubu
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin tarayya ta ce bikin ranar dimokuraɗiyya na bana zai ba da damar nuna nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A sanarwar da sakataren gwamnatin tarayya ya fitar, ya ce za a fadi ci gaban da aka samu wajen ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da bunƙasa ci gaban ƙasa.
Sanata George Akume ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ƙaddamar da kwamitin tsakanin ma’aikatu (IMC) domin bikin ranar dimokuraɗiyya karo na 27 a Abuja.
Asali: Legit.ng