"Sun Karbi na Goro," Malamin Addini Ya Tona Asirin Masu Goyon bayan Tinubu a 2027

"Sun Karbi na Goro," Malamin Addini Ya Tona Asirin Masu Goyon bayan Tinubu a 2027

  • Fitaccen malamin addini daga Anambra, Chukwuemeka "Odumeje" Ohanaemere, ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan batun yunwa da halin da ƙasa ke ciki
  • Odumeje ya yi zargin cewa masu yabon gwamnatin na yin hakan ne saboda son rai, yana mai cewa shugabanni ya kamata su yi aiki domin jama'a ba kansu ba
  • Malamin ya buƙaci 'yan Najeriya su yi amfani da zaɓen 2027 wajen hukunta shugabanni, tare da neman a riƙa bayyana yadda ake kashe kuɗaɗen da aka karɓo bashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Anambra - Fitaccen malamin addini daga jihar Anambra, Chukwuemeka "Odumeje" Ohanaemere, ya soki gwamnatin Bola Tinubu, yana mai cewa shugabanni ya kamata su fifita muradun jama'a a kan bukatunsu na kashin kai.

Odumeje ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta a ranar Alhamis, inda ya yi tsokaci kan kalaman shugaban ƙasa game da matsalar yunwa da kuma halin da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

"Na ji kunya": Tinubu ya ba EFCC umarnin bude asusun gwamnatin Osun da aka rufe

Malamin addinin kirista, Odumeje ya soki gwamnatin Bola Tinubu
Fitaccen malamin addinin Kirista, Chukwuemeka Odumeje. Hoto: @prophet_odumeje
Source: Twitter

Malamin Kirista ya tabo batun shugabanci

Malamin ya yi zargin cewa wasu daga cikin masu yabon gwamnatin na yin hakan ne saboda wata fa'ida da suke samu, yana mai cewa hakan ba ya wakiltar muradin talakawan Najeriya, in ji rahoton Premium Times.

Odumeje ya ce duk wanda ya samu damar hawa mulki, ko ta hanyar zaɓe ko wata hanya da doka ta tanada, aikinsa shi ne kula da albarkatun ƙasa domin amfanin kowa.

Ya ce:

"Duk wanda ka ga yana yabon gwamnatin yanzu, ina ganin yana yin hakan ne saboda wata fa'ida da yake samu. Idan ka shiga gwamnati, aikinka shi ne ka kula da albarkatun Najeriya, ba harkokin iyalinka ko kasuwancinka ba.
"Dukiyar ƙasa ta kowane ɗan Najeriya ce, saboda haka shugabanni dole su yi amfani da ita wajen inganta rayuwar jama'a."

Malamin ya ce shugabanni ba su kamata su manta cewa jama'a ne suka ba su amanar jagoranci ba, don haka wajibi ne su yi aiki cikin gaskiya da riƙon amana.

Kara karanta wannan

Atiku da Peter Obi sun tafka kuskure, an cire su daga barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027

Ya yi kira kan zaɓen shekarar 2027

Odumeje, a cikin wani bidiyo da aka wallafa a Instagram, ya buƙaci 'yan Najeriya su yi amfani da zaɓen shekarar 2027 wajen tantance shugabanni da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka zaɓa suna kare muradun al'umma.

A cewarsa:

"A shekarar 2027 ne za mu nuna ko Najeriya ta kowa ce ko ta wasu tsirarun mutane. Mu ba yara ba ne, mu manya ne kuma muna da alhakin kare makomar 'ya'yanmu."

Ya kuma soki wasu gwamnoni da sanatoci da ke kare kalaman shugaban ƙasa kan cewa matsalar yunwa ta daɗe tana addabar Najeriya tun kafin hawansa mulki.

Primate Odumeje ya yi ikirarin cewa dukkan masu goya wa Tinubu baya kan zaben 2027 sun karbi cin hanci
Primate Chukwemeka Odumeje (hagu) da Shugaba Bola Ahmed Tinubu (dama). Hoto: @prophet_odumeje, @officialABAT
Source: Instagram

Ya aika sako ga gwamnatin tarayya

Malamin ya kuma yi magana kan yawan bashin da gwamnati ke karɓowa, yana mai cewa duk wani bashi da ake ci yana shafar rayuwar 'yan Najeriya da makomar al'ummomi masu zuwa.

Ya ce duk shugaban da ke jagorantar jama'a dole ne ya san yadda zai yi magana da su tare da bayyana yadda ake amfani da kuɗaɗen da aka karɓo.

Kara karanta wannan

EFCC ta rufe asusun gwamnatin jiha sukutum, an jefa gwamna a matsala dab da zabe

Odumeje ya jaddada cewa shugabanni suna wakiltar jama'a ne kawai, ba mallakar ƙasa suke yi ba, saboda haka dole su gudanar da mulki cikin gaskiya, rikon amana da bayyana gaskiya ga 'yan ƙasa.

Odumeje ya ce ya kusa barin duniya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Fasto Chukwuemeka Ohaneamere, da aka fi sani da Odumeje, ya yi wani hasashe wanda ya bayyana cewa ya kusa mutuwa.

Dan shekara 43 din wanda ya samar da Mountain of Holy Ghost Intervention and Deliverance Ministry ya ce dalilin zuwan shi duniya ya kammala kuma zai mutu nan ba da jimawa ba.

Primate Odumeje wanda ya bayyana haka ga mabiyansa ya ce ya tattauna da dan shi ya kuma gaya masa ya shirya zama jagoran iyalin shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com