PDP Ta Jijjiga, Ƴan Majalisar Wakilai 6 Sun Yi Mata Tutsu, Sun Fice daga Jam'iyyar
- Gwamna Seyi Makinde ya ƙara nuna ƙarfinsa a siyasar Oyo bayan karɓar wasu ‘yan majalisar wakilan tarayya shida
- ‘Yan majalisar sun bayyana cewa rikicin cikin gida da takaddamar shugabanci a PDP ne suka sa suka sauya sheƙa
- A zaman majalisar, an karanta wasiƙun sauya sheƙa 13, inda PDP ta rasa wasu mambobi amma ta kuma samu sababbi daga APC da LP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sake samun karuwa bayan ƴan majalisar wakilai sun bar PDP.
Makinde ya sake nuna tasirinsa a harkokin siyasa bayan mambobi na Majalisar Wakilai shida da ke biyayya gare shi sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APM.

Source: Facebook
A lokacin da Majalisar Wakilai ta koma zaman aiki bayan hutun Sallah, Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, ya karanta wasiƙu 13 da ke sanar da sauya sheƙar ‘yan majalisa daga jam’iyya zuwa wata, cewar Punch.
Gwamna Makinde yana takara a APM
Ana tuna cewa Makinde ya fice daga PDP zuwa APM makonnin da suka gabata, kuma tuni ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar.
‘Yan majalisar wakilan Oyo da suka sauya sheƙa zuwa APM sun haɗa da Anthony Adebayo, Adedeji Olajide, Sunday Makanjuola, Oyedeji Oyeshina, Fola Oyekunle da Adigun Adekunle.
A cikin wasiƙunsu na sauya sheƙa, ‘yan majalisar sun bayyana cewa rikicin cikin gida da takaddamar shugabanci a PDP ne ya sa suka zaɓi wata sabuwar hanyar siyasa domin cimma burinsu na 2027.
Da wannan sauyi, Gwamna Makinde ya yi nasarar jawo mambobi shida daga cikin ‘yan majalisar wakilai 14 na Oyo zuwa jam’iyyar APM.

Source: Facebook
PDP ta sake rasa jiga-jiganta a Bauchi
A Bauchi, ɗan majalisa Auwalu Gwalabe ya fice daga PDP zuwa APM, yayin da Shehu Dalhatu mai wakiltar Faskari/Kankara/Sabuwa a Katsina ya bar APC ya koma PDP.
A cikin wasiƙarsa ta sauya sheƙa, Dalhatu ya ce:
"Bayan nazari mai zurfi kan matsalolin da ke APC da kuma tuntubar al’ummata, na yanke shawarar komawa PDP.”
Haka kuma, ɗan majalisar Delta, Etanabene Benedict, ya fice daga LP zuwa PDP, yana mai cewa rikicin cikin jam’iyyar LP ne ya haifar da matakin, cewar Daily Post.
PDP ta kuma samu wani ɗan majalisa, Alex Egbona, wanda ya fice daga APC zuwa PDP, amma ya jaddada cewa biyayyarsa ga mazabarsa da majalisar ba za ta canza ba.
An zargi gwamna da shirya sace dalibai
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yi zargin cewa an shirya sace ɗalibai da malamai a wasu makarantun jihar Oyo ne da gan-gan.
Fayose ya yi zargin cewa gwamnatin Gwamna Seyi Makinde ce ta shirya sace su a matsayin wani yunƙuri na ƙoƙarin bata sunan Bola Ahmed Tinubu.
Tsohon gwamnan ya ce ba a yin adalci wajen zargin shugaban kasa da matsalolin tsaro, alhali gwamnatocin jihohi ya kamata a rika jefa wa tambayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

