Buratai Ya Yi Tone Tone kan 'Yan Siyasa game da Rashin Tsaron Najeriya

Buratai Ya Yi Tone Tone kan 'Yan Siyasa game da Rashin Tsaron Najeriya

  • Tsohon hafsan sojin kasa, Tukur Buratai, ya daura alhakin ci gaba da matsalar tsaro kan sauye-sauyen gwamnati da kuma ayyukan wasu ‘yan siyasa
  • Buratai ya ce wasu ‘yan siyasa na anfani da matsalar tsaro domin cimma muradunsu na siyasa da kuma samun riba ta kashin kai, musamman a karkara
  • Ya yi magana ne ne yayin da ake cigaba da tattaunawa kan sace daliban da wasu 'yan bindiga suka yi a jihar Oyo da ke Kudancin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon babban hafsan sojin kasa, Tukur Buratai, ya ce karuwar matsalolin tsaro, ‘yan bindiga da sace ɗalibai a makarantu na da alaƙa da sauye-sauyen gwamnati da kuma ayyukan wasu ‘yan siyasa.

Maganar tsohon hafsun sojan ta zo a daidai lokacin da 'yan ta'adda ke cigaba da kai hare-hare yankuna da dama na Najeriya.

Kara karanta wannan

"Za a iya gano su"; Buratai ya dauko batun 'yan bindigan da ke fitowa a bidiyoyi

Tsohon shugaban sojin kasa, Tukur Buratai
Tukur Buratai a wajen wani taro. Hoto: Tukur Buratai
Source: Twitter

Buratai ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar TVC News, inda yake tsokaci kan sace ɗalibai da malamai da aka yi kwanan nan a jihar Oyo.

Tsaro: Buratai ya zargi 'yan siyasa

A cewar Buratai, wasu ‘yan siyasa sun daɗe suna ɗaukar nauyi da tallafa wa masu aikata laifuffuka domin cimma manufofinsu, amma daga baya waɗannan mutane sukan rikide su zama ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga.

“Abin takaici, gaskiyar magana ita ce wasu ‘yan siyasa suna anfani da ayyukan waɗannan ‘yan ta’adda,”

In ji shi.

Tsohon hafsan sojin ya ce matsalar tsaro kan ƙara muni ne a lokutan sauya gwamnati, lokacin da ayyukan tsaro kan fuskanci tangarda da matsalolin kuɗi.

Ya ce ana lura cewa ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga kan ƙara kai hare-hare musamman a lokacin zaɓe ko kuma lokacin da ake canja gwamnati daga wata zuwa wata.

The Sun ta rahoto ya ce:

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

“Za ka ga cewa waɗannan ‘yan ta’adda suna da wata al’ada ta musamman, musamman idan akwai harkokin siyasa ko lokacin sauyin gwamnati,”

Hanyar magance matsalar tsaro

Domin magance matsalar tsaro, Buratai ya ba da shawarar a samar da cikakkiyar dabara da za ta haɗa da karkasa ayyukan yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa hukumomin tsaro da kuma dawo da amincewar jama’a.

Ya yi kira da a kafa rassan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro a matakin jihohi, tare da samar musu da kayan sa ido na zamani da sauran kayan aiki.

Tukur Buratai a ofis
Lokacin da Tukur Buratai ke cikin ofis. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

Haka kuma ya bukaci a ƙara ɗaukar jami’ai aikin soja da ‘yan sanda, a inganta shirye-shiryen horo da kuma kyautata jin daɗin jami’an tsaro.

Baya ga haka, Buratai ya bukaci gwamnatin tarayya ta ƙara kusantar al’ummomin da matsalar tsaro ta shafa ta hanyar kai ziyara da kuma ci gaba da tattaunawa da su domin ƙarfafa musu gwiwa da haɗin kai da hukumomin tsaro.

Tsaro: APC ta nemi Makinde ya sauka

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar APC a jihar Oyo ya bukaci Gwamna Seyi Makinde ya sauka saboda matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

APC ta yi magana ne bayan Makinde ya ce karfin ceto daliban da aka sace a jihar na karkashin gwamnatin tarayya ba shi kadai ba.

A kan haka ne jam'iyyar APC adawa a jihar ta ce gwamnan ya nuna rashin kwarewa wajen fuskantar matsalolin da suka addabi Oyo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng