'Yan Bindiga Sun Aikata Ta'asa, Sun Sace Shugaban Makaranta da Dalibai Masu Yawa a Oyo

'Yan Bindiga Sun Aikata Ta'asa, Sun Sace Shugaban Makaranta da Dalibai Masu Yawa a Oyo

  • Yan bindiga sun kai farmaki wata makarantar sakandire da ke yankin Ahoro-Esinele a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo da safiyar yau Juma'a
  • Maharan sun harbi malami daya, sun sace shugaban makaranta da wasu dalibai da har yanzu ba tantance yawansu ba
  • Rundunar yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da aukiwar lamarin, inda ta tura dakaru zuwa yankin domin ceto duka wadanda aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo, Nigeria - ‘Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a yankin Ahoro-Esinele da ke karamar hukumar Oriire a jihar Oyo.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace shugaban wata makarantar sakandare tare da wasu dalibai da ba a tantance yawansu ba har kawo yanzu.

Jihar Oyo.
Taswirar jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Punch ta ruwaito cewa rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne tsakanin karfe 8:00 zuwa 9:00 na safiyar yau Juma’a a makarantar Community High School da ke Ahoro-Esinele.

Kara karanta wannan

"Babu hujja," Sojojin Najeriya sun yi magana kan zargin kashe fiye da mutane 100 a Zamfara

Yan bindiga sun kai hari makaranta a Oyo

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ayanlade Olayinka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da tsakar rana a yau Juma'a, 15 ga watan Mayu, 227.

Ya tabbatar da cewa yan bindigar sun kutsa cikin harabar makarantar tare da yin awon gaba da wasu dalibai wadanda har yanzu ba a tantance yawansu ba, da shugaban makarantar, Misis Rachael Alamu.

Sanarwar ta ce:

“‘Yan bindiga sun kai hari yankin Ahoro-Esinele da ke karamar hukumar Oriire a jihar Oyo, inda suka sace shugaban wata makarantar sakandare da kuma wasu dalibai da ba a san yawansu ba.”

Yadda yan bindiga suka yi ta'asa a harin

A cewarsa, wani mazaunin yankin ya bayyana cewa maharan sun kuma harbi wani malami a makarantar yayin harin, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

“Majiyar ta kuma ce an harbi wani malami a lokacin harin, amma har yanzu ba a tabbatar da irin raunukan da ya samu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta magantu da ake zargin harin jirgi ya kashe yan kasuwa 100

“Rahoton da muka samu ya nuna cewa ‘yan bindigar sun tsere da shugaban makarantar a cikin motarta zuwa wani daji da ke iyaka da yankin.
“Mazauna yankin sun ce ofishin ‘yan sanda mafi kusa yana da nisa, lamarin da ya jinkirta daukar matakin gaggawa,” in ji Olayinka.
Yan sanda.
Dakarun rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce kwamishinan ‘yan sanda ya tura jami’ai zuwa yankin domin tantance halin da ake ciki tare da gudanar da aikin ceto wadanda aka sace.

Boko Haram ta sace dalibai a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai hari da sanyin safiya a wasu makarantu da ke jihar Borno.

'Yan ta'addan sun sace adadin ɗaliban da ba a tantance ba na makarantar firamare da karamar sakandare ta Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.

Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Borno, Rt Hon. Abdullahi Askira, wanda shi ma ɗan Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ne, ya tabbatar da harin da ’yan ta’addan suka kai

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262