Yan Bindiga Sun Sace Yayar Tsohon Minista da ’Ya’yanta Tagwaye Guda 2
- Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da yar tsohon Ministan makamashi a Najeriya tare da tagwayen ‘ya’yanta a jihar Oyo da sanyin safiyar yau
- Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki lokacin da take kai ‘ya’yanta makaranta, inda suka tafi da su da karfi ba tare da jin tausayin jama’a ba
- Iyalan Adelabu sun tabbatar da lamarin, sun nemi addu’a da taimakon jama’a, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike domin ceto wadanda aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Ana tsaka da jimami bayan sace dalibai da malaman makaranta da bindiga suka yi a Oyo, mahara sun sake tafka ta'asa.
An sace yayar tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, tare da tagwayen ‘ya’yanta a birnin Ibadan.

Source: Twitter
Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne yayin wani mummunan hari na ‘yan bindiga wanda ya tayar da hankulan al'umma, cewar Punch.
Yadda aka sace yayar tsohon minista a Najeriya
Wata shaida ta ce lamarin ya faru ne a yankin Challenge, inda aka kai harin safiyar Laraba yayin da take kan hanyarta zuwa makaranta da ‘ya’yanta.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi amfani da karfi wajen kwashe ta tare da tagwayen ‘ya’yanta, masu shekaru kimanin shekara 12.
Da yake tabbatar da lamarin a wata sanarwa, daya daga cikin masu taimaka wa tsohon ministan makamashi, Adebayo Adelabu, Femi Awogboro, ya ce:
“Iyalan Adebayo Adelabu, tsohon Ministan Wuta kuma fitaccen mai neman tikitin gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Oyo, suna tabbatar da garkuwa da yayarsa, Olaide Busayo Adegoke John-Paul, tare da tagwayen ‘ya’yanta, Peter da Paul, a farkon safiyar Laraba, 3 ga Yuni, 2026.
“An sace Olaide Busayo Adegoke John-Paul, mai shekaru 43 da misalin karfe 7:30 na safe yayin da take kan hanyarta na kai ‘ya’yanta makaranta a Ibadan.
Haka kuma masu garkuwar sun tafi da tagwayen ‘ya’yanta masu shekaru 12 da karfi, wadanda ke tare da ita a lokacin lamarin.”

Source: Original
Matakin da jami'an tsaro suka dauka
Ya ce jami’an tsaro sun fara aiki, kuma ana sa ran gano wadanda suka aikata wannan mummunan laifi tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su.
Iyalan sun bukaci jama’a su kwantar da hankali, su guji yada jita-jita, tare da neman addu’o’i da hadin kai a wannan mawuyacin lokaci.
Sun kuma roki duk wanda ke da bayanai da zai taimaka wajen gano wadanda aka sace ya mika su ga hukumomin tsaro nan take, cewar TheCable.
Sace dalibai: Iyayen yara sun ba gwamnati kunya
A wani labarin mai kama da wannan, wasu yan bindiga sun kai hari a jihar Oyo inda suka sace dalibai da malaman makaranta yayn wani farmaki.
Sarkin yankin Yawota da aka sace dalibai da dama a jihar Oyo ya bayyana yadda iyayen yaran suka ki ba da hadin kai da gwamnati ta ba su kyauta.
Iyayen ɗalibai da malamai da aka sace a Oriire da ke Oyo sun ƙi karɓar shinkafa da kuɗi daga gwamnati, suna neman a dawo musu da yaransu.
Asali: Legit.ng

