Yadda Iyayen Yara da Aka Sace Suka Ki Karbar Kudi, Shinkafa daga Gwamnati

Yadda Iyayen Yara da Aka Sace Suka Ki Karbar Kudi, Shinkafa daga Gwamnati

  • Sarkin yankin Yawota da aka sace dalibai da dama a jihar Oyo ya bayyana yadda iyayen yaran suka ki ba da hadin kai da gwamnati ta ba su kyauta
  • Iyayen ɗalibai da malamai da aka sace a Oriire da ke Oyo sun ƙi karɓar shinkafa da kuɗi daga gwamnati, suna neman a dawo musu da yaransu
  • Sarkin, Mai martaba Emmanuel Alade ya ce maharan sun kai farmaki suna harbe-harbe, suka sace ɗalibai da malamai tare da kashe wasu mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yawota, Oyo - Sarkin Yawota da ke ƙaramar hukumar Oriire a Oyo, Emmanuel Alade, ya bayyana cewa iyayen yaran da aka sace sun ƙi tallafin gwamnati.

A wata hira ta bidiyo, Alade ya ce jami’an gwamnati sun kai shinkafa da kuɗi zuwa al’ummar domin rage radadin abin da ya faru.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace yayar tsohon ministan Tinubu da 'ya'yanta tagwaye

Rashin tsaro ya tayar da hankula a Oyo
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da aka sace dalibai. Hoto: Seyi Makinde.
Source: Facebook

Iyaye, malamai sun ki karbar tallafin gwamnati

Sai dai iyayen yaran da malamai da aka sace sun ƙi karɓar tallafin, suna jaddada cewa abin da suke so shi ne a dawo musu da yaransu, cewar rahoton Punch.

Basaraken ya ce ya ga wasu mutane da ake zargi kafin jin karar harbe-harbe da ta tabbatar da farmakin da maharan suka kai.

Ya bayyana cewa maharan sun kutsa cikin al’ummar, suna ta harbe-harbe, inda suka sace ɗalibai da malamai da dama daga makarantu uku.

A cewarsa, ƙananan yara da malamai ne aka yi garkuwa da su, yayin da wani mataimakin shugaban makaranta ya rasa ransa.

Ya ce:

"Ina zaune a nan lokacin da na ga sun wuce, amma ban san su ko kaɗan ba.
"Ba da jimawa ba bayan nan, muka fara jin karar harbe-harbe. Sai aka ce 'yan bindiga sun shiga al'ummar, kowa ya rika guduwa. Mutumin da ya je domin ganin su kuwa sai suka harbe shi har lahira."

Kara karanta wannan

Buratai ya yi tone tone kan 'yan siyasa game da rashin tsaron Najeriya

Yadda iyayen yara da aka sace suka ƙi karbar kudi da shinkafa daga gwamnati
Taswirar jihar Oyo da ƴan bindiga suka sace dalibai da dama. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka sace dalibai da malamai a Oyo

An kai harin ne ranar 15 ga Mayu, 2026, a yankunan Esiele, Yamota da Alawusa, inda sama da mutum 40 suka shiga hannun maharan, in ji Daily Post.

Bidiyoyi sun nuna wasu malamai da aka sace suna roƙon a kawo musu dauki, yayin da aka dauke wani malamin lissafi yayin harin da aka kai.

Lamarin ya tayar da hankalin jama'a, inda malamai suka shiga yajin aiki, yayin da gwamnatin tarayya ta umarci ƙara ƙaimi wajen ceto waɗanda aka sace.

Rashin tsaro: An bukaci Makinde ya yi murabus

A wani labarin, an ji cewa jam’iyyar APC reshen Oyo ta bukaci Gwamna Seyi Makinde ya yi murabus daga mukaminsa idan har yana ganin ba shi da ikon kare rayuka.

Matsayar jam’iyyar ta biyo bayan kalaman da Makinde ya yi yayin jawabin karɓar takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APM a birnin badan da ke Oyo.

An ruwaito Makinde yana cewa ba shi da abubuwa da yawa da zai iya yi wajen tabbatar da ceto ɗaliban makaranta da sauran jama'an da aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.