Sanatocin Arewa Sun Haɗa Kai, Sun Yaba wa Tinubu duk da Matsalolin Tsaro da Ake Ciki

Sanatocin Arewa Sun Haɗa Kai, Sun Yaba wa Tinubu duk da Matsalolin Tsaro da Ake Ciki

  • Sanatocin yankin Arewacin Najeriya ta yabawa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro kan nasara a yaƙi da ta'addanci a kasar
  • Sanata Abdulaziz Musa Yar'Adua ya ce hadin gwiwar 'yan sanda, DSS, NSCDC, sojoji da masu tsaron sa-kai tare da bayanan jama'a sun taimaka wajen nasarar aikin
  • Sanatocin sun jajanta wa iyalan wadanda suka rasu, sannan suka bukaci jama'a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai domin yaki da rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa Sanatocin Arewa sun yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hukumomin tsaro a Najeriya.

Sanatocin sun yi yabon ne saboda nasarar kubutar da mutanen da aka sace daga al'ummar Woro da ke Kwara ba tare da sun ji rauni ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana da limaman Katolika suka cire tsoro, sun ja da Tinubu

Sanatocin Arewa sun yaba wa Tinubu
Sanata Abdul'aziz Yar'Adua daga jihar Katsina. Hoto: Senator Abdul'aziz Yar'Adua.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Sanata Abdulaziz Musa Yar'Adua, ya fitar a Abuja ranar Alhamis, cewar Tribune.

Sanatan ya kuma taya gwamnatin Kwara da al'ummar Woro murnar samun nasarar ceto mutanen.

Da yake magana a madadin sanatocin jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya, Yar'Adua ya yabawa Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, DSS, NSCDC, sojojin Najeriya da masu tsaron sa-kai saboda hadin gwiwarsu.

Ya ce wannan nasara ta nuna muhimmancin hadin kai tsakanin hukumomin tsaro da kuma samun sahihan bayanan sirri daga al'ummomi wajen magance matsalar rashin tsaro.

Yar'Adua ya ce jajircewa, kwarewa da hadin gwiwar hukumomin tsaro ne suka tabbatar da nasarar aikin ceto, abin da ya nuna karfin aiki tare wajen kare rayuka.

Majalisar ta kuma yabawa Shugaba Tinubu bisa samar da goyon bayan siyasa da albarkatun da suka bai wa hukumomin tsaro damar ci gaba da yaki da masu aikata laifuka.

A cewarsa, saurin daukar matakin gwamnatin tarayya da goyon bayan da ta bayar sun taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da an kubutar da wadanda aka sace cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sada Idi Abasu Aiki da wasu 'yan bindiga 60 da Mahaliccinsu a Katsina

Duk da murnar nasarar ceto, sanatocin sun jajanta wa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu yayin aukuwar lamarin, tare da yi musu addu'ar samun rahama.

Sun kuma bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin Kwara su tallafa wa iyalan mamatan domin rage musu radadin rashin da suka yi.

Har ila yau, Majalisar ta bukaci mazauna yankunan su ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro ta hanyar ba su sahihan bayanai cikin lokaci, tana mai cewa hakan na da matukar muhimmanci wajen dakile rashin tsaro.

Sanatocin sun sake jaddada kudurinsu na ci gaba da goyon bayan duk wani yunkuri da zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin Arewa, tare da yi wa al'ummar Woro addu'ar samun zaman lafiya mai dorewa.

Yar'adua ya karyata shirin barin APC

Kin ji cewa Sanata Abdulaziz Musa Yar'adua ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki.

Ya bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a ciki domin har yanzu shi cikakken mamba ne a jam'iyyar APC.

Sanatan mai wakiltar Katsina ta Tsakiya ya bayyana cewa ba kowane mai suna Yar'adua ba ne yake da alakar siyasa da shi.

Kara karanta wannan

Kosan Waka: An fitar da lokacin jana'izar fitaccen mawakin Gwamnan Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.