Fusatattun Mutanen Gari Sun Hallaka Dan Acaba kan 'Karyar' Harin Yan Bindiga
- Rundunar ‘yan sandan Legas ta kama mutum 15 bayan kisan wani matashin ɗan acaba sakamakon jita-jitar kutsen cewa ‘yan bindiga sun kutsa garin
- Matasan yanki sun yi wa mamacin kisan gilla bayan sun yi zargin cewa ɗan bindiga ne daga kabilar Fulani bayan an samu rahoton karya cewa sun kai hari
- ‘Yan sanda sun ce babu wani hari ko mamayar ‘yan bindiga a Ibeju-Lekki, Imota, Oke-Afo ko wani yanki na Legas kuma an yi wa 'dan acaban karya ne kawai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da kama mutane 15 da ake zargi da hannu a kisan wani matashin mai sana’ar acaba bayan ya faɗa tarkon jita-jitar cewa ‘yan bindiga sun mamaye wasu yankuna na jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas, CSP Abimbola Adebisi, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 1 ga watan Mayu, 2026.

Source: Twitter
A ruwayar The Cable, CSP Abimbola Adebisi ta ce rahotannin da suka bazu a kafafen sada zumunta na cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun mamaye yankunan Ibeju-Lekki, Imota, Oke-Afo da sauran wurare a jihar Legas, tare da kai hari kan makarantu da yara, ƙarya ne marar tushe.
Yan sandan Legas sun yi kame
Daily Post ta kawo labari cewa CSP Abimbola Adebisi ta bayyana cewa irin waɗannan saƙonni na ƙarya na haifar da fargaba da rudani a tsakanin jama'a.
Sanarwar ta ce:
“Zarge-zargen da ke cikin saƙonnin da ake yaɗawa ƙarya ne kuma marasa tushe, waɗanda aka ƙirƙira domin haddasa tsoro da firgici a tsakanin mazauna yankunan.”
Ta ƙara da cewa:
“A halin yanzu babu wata matsalar tsaro, mamaya ko wani shiri na kai hari ga makarantu ko al’ummomi a Ibeju-Lekki, Imota, Oke-Afo ko wani sashe na jihar Legas.”
Ana tsaron makarantun Legas
Adebisi ta tabbatar da cewa makarantu a faɗin jihar na ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da sintiri da sanya ido a yankuna daban-daban.
Kakakin ‘yan sandan ta bayyana cewa wannan jita-jita ta haifar da asarar ran bawan Allah, wanda abu ne da za a iya kauce masa baki daya.
A cewarta, wasu matasan yankin sun ɗauki matakin kai masa hari bayan sun yi imanin cewa ‘yan bindiga sun shiga yankinsu.

Source: Original
Ta ce:
“Wasu matasan al’umma, bisa wannan jita-jita da ba a tantance ba cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankin, sun zarge shi da kasancewa ɗan bindigar Fulani, sannan suka kai masa hari har ya mutu.”
Adebisi ta ce an kuma sace babur ɗinsa, yayin da daga baya aka gano gawarsa a cikin wani fadama da ke yankin. Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa an kama mutane 15 da ake zargi da hannu a lamarin kuma ana ci gaba da bincike.
Yan sanda sun ba Sowore umarni
A baya, mun wallafa cewa rundunar yan sanda ta umarci dakarunta su kama dan gwagwarmaya kuma dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore a duk inda suka gan shi a jihar Legas.
Kwamishinan yan sandan jihar, Olorundare Jimoh ya ce sun samu labarin shirin da Sowore ya yi na tayar da zaune tsaye da sunan zanga-zanga ta karkashin kungiyar Take It Back Movement.
Sai dai jami’an ‘yan sanda na sashin tarwatsa tarzoma da na Rundunar Task Force sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da ke adawa da wasu ayyukan gwamnati.
Asali: Legit.ng

