Rashin Tsaro: Jam'iyyar APC Ta Bukaci Gwamna Seyi Makinde Ya Yi Murabus
- Jam’iyyar APC reshen Oyo ta bukaci Gwamna Seyi Makinde ya yi murabus daga mukaminsa idan har yana ganin ba shi da ikon kare rayuka
- Matsayar jam’iyyar ta biyo bayan kalaman da Makinde ya yi yayin jawabin karɓar takarar shugaban ƙasa ta jam’iyyar APM a Ibadan
- An rawaito Makinde yana cewa ba shi da abubuwa da yawa da zai iya yi wajen tabbatar da ceto ɗaliban makaranta da sauran jama'an da aka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Jam’iyyar APC a Jihar Oyo ta soki Gwamna Seyi Makinde kan kalamansa game da halin tsaro a jihar, tana mai cewa bai fahimci nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗaura wa gwamnoni ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar, Olawale Sadare, ya fitar a Ibadan, APC ta yi watsi da ikirarin Makinde cewa yana fuskantar ƙalubale wajen magance matsalar tsaro saboda dukkan tsarin tsaro yana ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan
2027: Babachir Lawal ya rikita lissafin Atiku Abubakar, ya fice daga jam'iyyar ADC

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa jam’iyyar ta bayyana kalaman gwamnan a matsayin kololuwar rashin sanin makamar aiki, rashin gaskiya da kuma gazawa mai tsanani.
APC na so Seyi Makinde ya sauka
APC ta ƙara da cewa ya kamata Makinde ya yi murabus ya bar mataimakinsa ya kammala sauran shekara guda da ta rage masa a wa’adin mulkinsa.
“Shugabanni masu son zuciya irin Makinde babbar barazana ce ga ci gaba da bunƙasar al’ummar Najeriya, kuma yana da muhimmanci masu zaɓe su guje musu a zaɓuɓɓuka masu zuwa,”
In ji sanarwar.
An ce gwamnan ya bayyana a jawabin karɓar takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APM cewa ba shi da abubuwa da yawa da zai iya yi domin ceto ɗaliban makarantar da sauran mutanen da ‘yan bindiga suka sace.
Magana kan 'yan sandan jihohi
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Makinde ya sake jaddada kira a kafa ‘yan sandan jihohi bayan sace malamai da ɗalibai a makarantu uku da ke Ƙaramar Hukumar Oriire.
Gwamna Seyi Makinde ya ce lamarin ya sanya wannan lokaci ya zama mai wahala gare shi da kuma jihar baki ɗaya.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya ta bai wa majalisun dokokin jihohi damar samar da tsarin ‘yan sandan jihohi maimakon barin wannan nauyi ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda kaɗai.
Sai dai APC ta yi masa martani da cewa:
“Makinde bai taɓa ganin wata matsala a cikin kundin tsarin mulkin ƙasa ba lokacin da ya rantse sau biyu zai kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
"Ya yi amfani da ƙarfin ofishinsa wajen sarrafa iko, albarkatu da mutane ba tare da wata ƙorafi ba har sai yanzu da ya fuskanci babban ƙalubale wanda ya samo asali daga rashin ƙwarewa, rashin sanin makamar aiki da kuma son kai."

Source: Original
An yi zanga-zanga a Oyo
A wani labarin, mun kawo muku cewa masu fafutuka a kungiyar Take It Back Movement sun gudanar da zanga-zanga a jihar Oyo.
Daruruwan matasa ne suka cika tituna a birnin Ibadan domin nuna damuwar su kan sace dalibai da malamai a wasu makarantun jihar.
Masu zanga-zangar sun nuna damuwa kan yadda ake cigaba da tsare dalibai da malaman duk da cewa akwai yara kanana a cikinsu.
Asali: Legit.ng
