Minista a Isra'ila na Zuga Netanyahu, Yana Neman a Fara Yi wa Amurka Bore

Minista a Isra'ila na Zuga Netanyahu, Yana Neman a Fara Yi wa Amurka Bore

  • Wani minista mai tsattsauran ra'ayi a Isra'ila ya bukaci Firaminista Benjamin Netanyahu ya fara yi wa Amurka da bukatunta bore kan yakin Lebanon
  • Iran dai ta kafe a kan cewa babu maganar sulhu matukar Isra'ila ba ta daina kai harin ta'addanci wasu sassan Lebanon da ake ganin tana neman mamaye wa ba
  • Kwatsan, sai ga kalaman Ministan a lokacin da ake samun sabani tsakanin gwamnatin Isra'ila da Amurka kan yadda ake tafiyar da rikicin yankin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Isra'ila – Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila mai tsatstsauran ra'ayi, Itamar Ben-Gvir, ya tayar da kura bayan ya bukaci Firaminista Benjamin Netanyahu ya daina bin umarnin Amurka tare da nuna turjiya ga duk wani matsin lamba daga Washington.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun yi watsi da tayin N100,000 a matsayin mafi karancin albashi

Ya bayyana haka ne a dai-dai lokacin da ake samun musayar kalamai tsakanin Amurka da Isra'ila game da harin da sojojin IDP ke kai wa sassan Gabas ta Tsakiya.

Ana son Isra'ila ta fara yi wa Amurka bore
Shugaban Amurka Donald Trump (hagu) da Firayin Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu (dama). Hoto: Chip Somodevilla and Ronen Zvulun / POOL / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da kafar Aljazeera ta wallafa, Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga Netanyahu da ya fifita muradun Isra'ila fiye da bukatun Amurka, yana mai cewa lokaci ya yi da ƙasar za ta riƙa yanke hukuncinta ba tare da dogaro da ra'ayin ƙawayenta ba.

Kiran Ministan Isra'ila ga Netanyahu

The Tiimes of Israel ta wallafa cewa Itamar Ben-Gvir, ya soki sanarwar da Trump ya yi na dakatar da hare-haren da Isra’ila ta shirya kai wa yankunan Kudancin birnin Beirut, yana mai cewa “lokaci ya yi da za a ce wa Trump a’a.

Ya bayyana cewa:

“Lokaci ya yi da za a yi abin da ya wajaba, kuma abin da ake bukata shi ne a kai wa Hezbollah hari, a bai wa mayaƙanmu damar gudanar da ayyukansu, sannan a dawo da tsaro a yankin Arewa.”

Ya kuma yi kira ga Firaministan Isra’ila da ya ƙi amincewa da matsin lambar Amurka, ya kuma tsaya da kafarsa wajen maganar tsaron Isra'ila.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Kasar Iran ta gindaya sharadin cimma yarjejeniya da Amurka

A kalamansa:

“Mai Girma Firaminista, ka taɓa cewa firaminista mai ƙarfi yana cewa wa Shugaban Amurka ‘eh’ idan zai yiwu, kuma ‘a’a’ idan ya zama dole. Wannan ne lokacin da za a ce wa abokinmu, Shugaba Trump, ‘a’a’.”

Ana samun dambarwa tsakanin Amurka da Isra'ila

Kalaman ministan sun sake haskaka yadda ake samun saɓanin ra'ayi a tsakanin manyan abokan hulɗa biyu da suka dade suna aiki tare a fannin tsaro da siyasa.

Isra'ila na samun sabani da Amurka kan harin Lebanon
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

A kwanakin baya, rahotanni sun bayyana cewa Trump ya nuna rashin jin daɗinsa kan wasu matakan da Netanyahu ke ɗauka a yankin Lebanon, lamarin da ya nuna akwai rashin daidaito a wasu fannoni duk da kusancin da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Duk da haka, Netanyahu ya sha bayyana cewa Isra'ila za ta ci gaba da kare kanta daga duk wata barazana da take gani a matsayin haɗari ga tsaron ƙasar.

Iran ta sa sharadin sulhu da Amurka

A baya, mun kawo labarin cewa ana ci gaba da zaman jira domin ganin an cimma yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya wanda aka fara tun a karshen watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe kansila da babban darakta a Zamfara kwanaki 10 da sace su

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa akwai sharadin da sai an cika shi kafin a kulla wata yarjejeniya da kasar Amurka duk da kokarin da masu shiga tsakani kamar Pakistan ake yi wajen ganin an shawo kan yakin.

Hakazalika, Iran ta zargi Amurka da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a tsakanin bangarorin biyu a watan Afrilun 2026 yayin da ake samun rahotannin hari da mayar da martani a tsakanin kasashen biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng