Babban Sarki a Zamfara da Matawalle Sun Yi Addu'o'i ga Tinubu domin Samun Nasara

Babban Sarki a Zamfara da Matawalle Sun Yi Addu'o'i ga Tinubu domin Samun Nasara

  • Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya yabawa salon mulkin shugaban kasa, Bola Tinubu a cikin shekaru uku
  • Matawalle ya bayyana cewa nasarorin Shugaba Tinubu cikin karin wa’adi na shekaru hudu za su kai Najeriya matsayi mafi girma
  • A wajen taron addu’a da aka gudanar a fadar Sarkin Maradun, dubban mutane sun yi addu’o’i domin nasarar Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maradun, Zamfara - Karamin Ministan Tsaro, Bello Mohammed Matawalle, ya bayyana kwarin gwiwa kan gwamnatin Bola Tinubu.

Matawalle ya bayyana cewa nasarorin Shugaba Bola Tinubu a karin wa’adi na shekaru hudu za su kai Najeriya matsayi mafi girma fiye da gwamnatocin baya.

Matawalle ya jagoranci addu'o'i ga Tinubu
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da Bola Tinubu. Hoto: Dr. Bello Matawalle, Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Matawalle ya bayyana hakan ne a wani taron addu’a na musamman da aka gudanar a Fadar Masarautar Maradun da ke Zamfara, cewar The Sun.

Kara karanta wannan

'Atiku da Peter Obi su sake bude wa Tinubu kofa, APC na iya lashe zaben 2027'

Dubban mutane sun halarci addu'o'i ga Tinubu

A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar, dubban masu ibada sun halarci taron domin yi wa Shugaba Tinubu addu’a.

Mahalarta taron sun kuma yi addu’o’i domin zaman lafiya, ci gaban kasa da kuma samun nasara ga gwamnatin da ke mulki a halin yanzu.

Da yake jawabi a wajen taron, tsohon gwamnan Zamfara ya ce mutane da dama sun yi imanin cewa Allah ne ya kaddara Tinubu domin gyarawa da sake gina Najeriya.

Ya kara da cewa hawan Tinubu mulki ya nuna burin ’yan kasa na ganin an samu sauyi mai ma’ana wanda zai inganta rayuwar jama’a da ci gaban kasa.

Matawalle ya ce dole ne a ci gaba da addu’a domin ci gaban Najeriya tare da neman kariya daga duk wata makarkashiya da ake yi wa kasa, cewar Punch.

Matawalle ya yabawa salon mulkin Tinubu
Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Matawalle ya fadi muhimmancin yin addu'o'i

Ministan ya jaddada muhimmancin addu’a wajen bunkasa kasa, yana mai cewa addu’a wata hanya ce mai karfi da ke jawo taimakon Allah cikin harkokin shugabanci.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya cancanci tazarce saboda dukufa kan magance rashin tsaro,' APC

Ya bayyana cewa mutane a sassa daban-daban na Najeriya suna ci gaba da yi wa kasa da shugabanninta addu’a tare da fatan samun sakamako mai kyau.

Matawalle ya ce bambancin shugabanci yana kara bayyana a Najeriya, inda ya ce ana ganin sauye-sauye masu kyau karkashin jagorancin Shugaba Tinubu.

A nasa bangaren, Sarkin Maradun, Alhaji Muhammad Garba Tambari, ya bayyana Tinubu a matsayin wata ni’ima ga Najeriya tare da kira ga jama’a su ci gaba da addu’a.

Sarkin ya ce ana bukatar addu’a mai dorewa domin samun shiriyar Allah ga shugabanni da kuma dorewar zaman lafiya a fadin kasa baki daya.

Matawalle ya magantu kan nasarar Tinubu a 2027

Mun ba ku labarin cewa karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaben 2027.

Matawalle ya ce manufofin Tinubu sun fara haifar da daidaiton tattalin arziki, inganta tsaro da karfafa cibiyoyin gwamnati musamman a Arewa.

Ya gargadi ‘yan siyasa masu shirya rikici da cewa burinsu na kashin kai na iya lalata dimokuradiyya, yana kira da a goyi bayan shirye-shiryen gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.