Mutanen da Ke Tserewa 'Yan Bindiga Sun Nutse a cikin Kogi a Sokoto

Mutanen da Ke Tserewa 'Yan Bindiga Sun Nutse a cikin Kogi a Sokoto

  • Ƴan bindiga sun kai hari a ƙauyen Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto, inda ake fargabar mutane 21 sun mutu
  • Maharan sun sace mutum 37, yayin da dubban mazauna yankin suka tsere daga gidajensu sakamakon harin
  • Jiragen ruwa biyu sun kife yayin da mazauna ƙauyen ke ƙoƙarin tsallaka kogi domin tserewa, inda ake fargabar mutum 18 sun nutse

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Aƙalla mutum 21 ake fargabar sun mutu, yayin da aka sace wasu 37 bayan ƴan bindiga masu ɗauke da muggan makamai sun kai hari ƙauyen Tsamaye da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

Harin, wanda ya fara da misalin ƙarfe 9:00 na daren Litinin, 3 ga watan Agustan 2026 har zuwa bayan ƙarfe 3:00, ya kuma jawo ƙone gidaje biyu, satar dabbobi da kuma tarwatsa daukacin mazauna ƙauyen.

Kara karanta wannan

Gwamna ya bayyana yadda gwamnatin Tinubu ta jefa 'yan Najeriya cikin wahala

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Shaidu sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa dubban mazauna yankin sun tsere daga gidajensu sakamakon harin.

Mutane sun nutse yayin tserewa

Mazauna yankin sun ce harin ya haifar da wata mummunar matsala yayin da mutane da dama suka yi ƙoƙarin tsallaka wani kogi domin tserewa bayan samun labarin cewa ƴan bindigar na tafe.

A cewar mutanen yankin, jiragen ruwan da suka yi lodin mutane sun kife, inda ruwa ya kwashe kusan mutum 25, mafi yawansu mata da yara.

Yayin da aka ceto mutum bakwai da ransu, ana fargabar wasu 18 sun nutse, yayin da iyalai ke ci gaba da neman ƴan uwansu da suka ɓace.

An yi garkuwa da wasu mutane

Wani mazaunin yankin da ke shirin tserewa daga ƙauyen ya bayyana cewa ƴan bindigan da kansu sun tabbatar da cewa sun sace mutum 37 bayan ƴan uwan waɗanda aka sace sun kira wayoyinsu.

“Da muka kira ƴan uwanmu, sai ƴan bindigar suka ɗaga wayoyin suka ce su ne suka sace su. Sun ce sun tafi da mutum 37.” Inji shi

Kara karanta wannan

An kashe dan siyasa da 'yan bindiga suka kai kazamin hari Filato da dare

Ya ce yayin da aka sace wasu daga cikin mutanen a cikin ƙauyen, an kama wasu da dama a gonakin da ke kusa, inda suka je kwana saboda tsoron hare-haren da ake yawan kaiwa.

“Mafi yawancin waɗanda aka sace mata da yara ne. Ni da kaina na ga yadda ƴan bindigar suka ajiye jarirai uku a ƙasa yayin da suke tafiya da iyayensu mata.” In ji shi

An ce jami’an tsaro ba su kawo ɗauki ba

Mazaunin yankin ya koka cewa duk da sanar da jami’an tsaro game da harin, ba a kawo wani ƙarin ɗauki ba kafin maharan suka kammala abin da suka shirya.

“A harin da ya gabata mun ba su uzuri saboda ƴan bindigar sun kewaye su kuma suna harbe-harbe a kansu. Amma a wannan karon, an sanar da su tun da wuri, amma babu wanda ya zo ya cece mu.”

Mazauna ƙauyen sun watse

Wani mazaunin garin ya ce bayan harin, mutane ƙasa da 20 ne suka rage a ƙauyen, yayin da motoci sama da 100 suka kwashe mutanen da suka rasa matsugunansu daga yammacin ranar Litinin zuwa yanzu.

“Daga jiya zuwa yau, babu wanda ya ci abinci saboda firgici da tashin hankalin da harin ya jawo,” in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun saki sunayen mutane 2 da ke ba 'yan bindiga bayanai a Bauchi

Shugaban ƙaramar hukuma ya yi bayani

Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni, Ayuba Hashimu, ya tabbatar da faruwar hare-haren, amma ya ce bai iya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu ba.

“Lamarin ya faru, amma ni da kaina ban je wurin ba. Saboda haka, sai na tabbatar da alkaluman kafin in iya tabbatar da su,” in ji shi.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya tabbatar da harin, yana mai cewa an tura ƙarin jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya tare da hana sake kai hare-hare a ƙauyukan da abin ya shafa.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun fatattaki 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar 'yan sandan jihar Sokoto sun dakile wani hari da 'yan bindiga suka kai a jihar Sokoto.

Jami'an 'yan sandan sun kuma ceto tumaki 43 da 'yan bindiga suka sace daga kauyen Anada da ke karamar hukumar Binji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng