Sheikh Sani Rijiyar Lemo Ya Yi Kira ga Gwamnatin Abba kan 'Yan Daba a Kano
- A baya bayan nan, matasa 'yan daba na cigaba da hana mutane sakat a Kano, lamarin da ya jawo rufe hanyoyi da takaita zirga-zirga
- Malamin adinin Musulunci a Kano, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi kira ga gwamnatin jihar ta ta tashi tsaye wajen magance matsalar
- Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya bayyana cewa jami'an tsaro na matukar kokari a jihar, amma suna bukatar hadin kan 'yan siyasa matuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Yadda 'yan daba suka dawo kai farmaki kan al'umma a jihar Kano na cigaba da daukar hankalin al'umma a fadin Najeriya.
Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya bukaci gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta tashi tsaye wajen kawo karshen lamarin a Kano.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo ya yi ne a wani bidiyo da Dr Muhsin Ibrahim ya wallafa a shafinsa na X.
Malamin hadisin ya sake jan hankalin a shirin Fatwowin Rahma inda ya saba amsa tambayoyi game da addini da rayuwa da jama'a suke aiko masa.
Kiran Sani Rijiyar Lemo kan daba a Kano
A wata nasiha da ya yi wa gwamnatin jihar Kano, Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya bukaci a dauki matakin da ya dace domin kawo karshen 'yan daba.
Ya ce:
"Muna kara kira ga gwamnati, ta sake sa ido a kan sha'anin daba, sha'anin daba yana neman ya maida wannan jiha ta mu a ta koma hannun 'yan daba, su ke da dama su rufe titi, su rufe unguwa, su hana mutane sakat.
Malamin ya yi korafi da cewa abin takaici ne yadda wasu masu mulki ko 'yan siyasa ke amfani da 'yan daba domin cimma manufarsu.
Ya ce:
"An zo wani lokaci da wasu daga cikin masu mulki, wasu 'yan siyasa suna amfani da 'yan daba domin cimma manufarsu."
Illar da daba za ta yi a Kano
A nasihar da ya yi, malamin ya nuna cewa rikicin daba zai kawo koma baya ga jihar Kano ta fuskoki da dama matukar ba a kawo karshen shi ba.
Ya bayyana cewa amfani da 'yan daba tamkar kashe kai ne ko kashe jihar, ya ce duk wani alheri da za a kawo jihar za a iya datakar da shi idan aka fahimci haka halin jama'ar garin ya ke.
Sheikh Sani Umar Rijiyar Lemo ya yaba wa jami'an tsaro bisa yadda suke tashi tsaye waje yaki da daba, sai dai ya ce suna bukatar hadin kan sauran shugabanni domin cimma nasara.

Source: Facebook
An samu rahotanni da dama da suka tabbatar da cewa 'yan daba sun yi sace-sace, kashe-kashe da toshe hayoyi da dama a Kano a kwanan nan.
A shirin fatawowin rahama, shehin ya koka ganin har yau babu labarin matakin da aka dauka a kan wadanda suka yi aika-aikar nan a kasuwar waya.
Ga bayanin da malamin ya yi a bidiyo:
'Ana kashe mutane a Kano,' Comrade
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan takarar gwamna na jam'iyyar NDC a Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya koka kan kashe mutane a Kano.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar ya yi korafi ne a wani taron siyasa inda ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya gagara tsare rayukan jama'a.
Aminu Gwarzo ya kara da cewa akwai hare-haren 'yan bindiga da ake kaiwa a karamar hukumar Shanono wanda a yanzu ya fara shiga wasu yankuna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


