Gwarzo: "Adadin Kanawa da Ake Hallakawa a Gwamnatin Abba Ya Fara Yawa"

Gwarzo: "Adadin Kanawa da Ake Hallakawa a Gwamnatin Abba Ya Fara Yawa"

  • Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana cewa an rasa rayukan mutane da dama a karkashin gwamnatin Gwamna Abba
  • Hakazalika, ya zargi Gwamna Abba da gaza sauke nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar adawa ta NDC a Kano kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Aminu Abdussalam Gwarzo ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da gazawa wajen sauke nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar.

Aminu Gwarzo ya soki Gwamna Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf da Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wata hira da ya yi da tashar BBC Hausa.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya kadu da Allah ya yi wa tsohon kwamishina rasuwa a jihar Kano

Gwarzo ya soki gwamnatin Gwamna Abba

Abdussalam Gwarzo ya bayyana yanayin tsaro a Kano a matsayin abin fargaba, inda ya ce ya gurgunce fiye da kowane lokaci a tarihin baya-bayan nan.

"A karamar hukumar Tsanyawa, an kashe mutane da dama sannan aka kwashe dukiyoyinsu. Makamancin wannan lamari ya faru a karamar hukumar Shanono, kuma a halin yanzu yana faruwa a karamar hukumar Gwarzo."
"Masu laifi sun sha kai hare-hare a kauyuka, sun kwashe kayayyakikin mutane, sun kashe wasu mazauna jihar, sannan suka sace wasu. Wasu daga cikin wadanda aka sace ɗin suna tsare a hannun masu garkuwa da mutane sama da watanni shida.”

- Aminu Abdussalam Gwarzo

Gwarzo ya koka kan rashin tsaro

Ya ƙara yin zargin cewa ko a cikin ƙananan hukumomin da ke cikin kwaryar birni ma, an kashe mutane da dama a cikin makwannin baya-bayan nan.

“Allah ne kaɗai ya san adadin mutanen da aka kashe a cikin makwanni uku da suka gabata kawai. An yi ta karkashe mutane kai-tsaye. Ina zaman lafiyar yake? Me ya faru da alƙawarin cewa Kano za ta amfana da tsaro idan gwamnatin jihar ta tafi tare da Gwamnatin Tarayya?”

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

- Aminu Abdussalam Gwarzo

Aminu Gwarzo ya soki gwamnatin Abba
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo Hoto: Aminu Abdussalam Gwarzo
Source: Twitter

Aminu Abdussalam Gwarzo ya kuma bayyana wani lamari na baya-bayan nan wanda ya yi daidai da ranar rantsar da mataimakin gwamnan jihar.

“A daidai ranar da aka rantsar da mataimakin gwamnan, an kashe mutane biyar. Mun ga iyayensu suna kuka cikin baƙin ciki, kuma mun ga gawarwakin da idanunmu."
"Wasu daga baya sun rawaito cewa wani mutum ɗaya ya ƙara mutuwa, wanda hakan ya sanya adadin wadanda suka mutu ya kai shida. Ina tsaron yake? Ina APC take? Ina Gwamnatin tarayya take?”

- Aminu Abdussalam Gwarzo

Aminu Gwarzo ya yi zargi

Tsohon mataimakin gwamnan ya ba da hujjarsa cewa ƙalubalen tsaron jihar sun karu ne bayan da gwamnati ta ƙaddamar da tsarin nan nata na “Kano First”.

A cewarsa, an ari wannan taken ne daga tunanin siyasa na zamanin mulkin mallaka, kuma yana kwaikwayon manufar “America First” wadda ta shahara a ƙasar Amurka.

Gwamna Abba ya ce ya cika alkawura

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 game da Aminu Gwarzo, wanda zai yi wa NDC takarar Gwamnan Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana kokarin da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru uku da ya yi a mulki.

Abba Kabir ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cika kusan kashi 90 cikin 100 na alkawuran da ta ɗauka wa al’ummar jihar cikin shekaru uku na mulki.

A cewarsa, an samu ci gaba a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, samar da ruwa​, ababen more rayuwa da ƙarfafa matasa domin inganta rayuwar jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com