Abubuwa 4 game da Aminu Gwarzo, Wanda Zai Yi wa NDC Takarar Gwamnan Kano
Tsohon 'dan takarar shugaban kasa kuma jagoran NDC a jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bayyana tsohon mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam Gwarzo a matayin 'dan takarar gwamnan Kano.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tsallake tsohon 'dan takarar gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, sai ya mika takarar gwamnan Kano a zaben 2027 ga Aminu AbdulSalam Gwarzo.
Aminu AbdulSalam Gwarzo shi ne tsohon mataimakin gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf kafin sabanin siyasa ya gifta a tsakaninsu, lamarin da ya kai ga ya yi murabus.

Source: Twitter
A sanarwar da Kwankwaso ya wallafa da kansa a shafinsa na Facebook, ya tabbatar da cewa yanzu Gwarzo shi ne zai tsaya wa NDC wajen neman kujerar Gwamna.
Yana daga cikin fitattun 'yan siyasar jihar Kano da suka shafe shekaru suna hidima a fannoni daban-daban na gwamnati da siyasa.
Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwan da ya kamata a sani game da tsohon mataimakin gwamnan, ga su kamar haka;
1. Haihuwa da ilimin Aminu Abdussalam Gwarzo
An haifi Aminu Abdussalam Gwarzo a garin Gwarzo da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano, Najeriya. Ya fara karatu a makarantar firamare ta Gwarzo tsakanin 1966 da 1972, sannan ya halarci Kano Teachers College daga 1972 zuwa 1977.
Daga baya ya yi karatu a makarantar fasaha ta Kano inda ya samu takardun OND da HND, sannan ya kara ilimi a Bayero University Kano.
2. Gwarzo ya samu horo a kasashen waje
A bayanin da hadiminsa, Ibrahim Garba Shua'abu ya yi, ya ce Gwarzo ya halarci kwasa-kwasai na shugabanci da gudanarwa a cibiyoyin horo da ke Landan, daga ciki har da Royal Institution of Public Administration (RIPA) da Global Training Consulting (GTC).
Daga cikin takardun da ya samu akwai babbar difloma (HND) a fannin ilmin akanta da kuma OND a harkar aikin banki da ilmin tattali sannan yana da shaidar PG a harkar gudanarwa da tsare-tsaren al'umma.
3. A ina Aminu Gwarzo ya yi aiki?
A sauran bayanan da Legit ta samu, an gano aikinsa na farko a gwamnati ya fara ne a matsayin malami Firamaren Kara a shekarar 1977. Daga baya ya zama shugaban makarantar Firamaren Salihawa da ke Gwarzo.

Source: Facebook
Tsakanin shekarun 1988 zuwa 1994, ya rike mukamai daban-daban a Hukumar Tara Haraji ta jihar Kano, inda ya jagoranci sassa da yankuna daban-daban.
4. Siyasar Gwazo a Kano
Sanarwar da Ibrahim Shuaibu ya fitar wanda Ahmad Nura Bala Gwarzo ya wallafa a Facebook, ta ce an zabe shi shugaban karamar hukumar Gwarzo a shekarar 1996 sannan ya sake rike mukamin daga 1999 zuwa 2003.
A tsawon rayuwarsa ta siyasa, Gwarzo ya zama kwamishina a ma'aikatu daban-daban da suka hada da Ma'aikatar Ayyuka, Ma'aikatar Harkokin Gwamnati da kuma Ma'aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu.
Daga 2015 zuwa 2019, ya kasance babban mataimaki na musamman a bangaren harkokin majalisa ga tsohon gwamnan Kano kuma Sanata, Rabiu Musa Kwankwaso.
Aminu AbdulSalam Gwarzo ya taba zama mataimakin dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar PDP a zaben 2019.
Haka kuma ya kasance mataimakin shugaba na kasa na kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) daga 2000 zuwa 2002, sannan ya taba zama wakilin taron kasa na jam'iyyar PDP da shugaban kungiyoyi daban-daban na matasa da ma'aikata.
A 2019 da 2023 ya yi takarar mataimakin gwamnan Kano kuma ya rike ofishin daga Mayun 2023 zuwa Maris a 2026.
NDC: Kwankwaso ya ayyana dan takarar gwamnan Kano
A baya, mun ruwaito cewa Sanata Rabiu Kwankwaso da kaddamar da yan takarar NDC a ranar Juma'a, 29 ga Mayun 2026 domin su wakilci jam'iyyar a babban zaben 2027 da ke tafe.
Kwankwaso ya ayyana tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa NDC takarar gwamnan Kano, inda zai kara da tsohon mai gidansa.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kuma fadi matsayin da tsohon mataimakin gwamnan Kano, Dr Nasiru Yusuf Gawuna zai nema a karkashin tafiyar NDC Kwankwasiyya a babban zaben.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


