Matsalar Ruwan Sha Ta Yi Katutu a Jihar Gombe, Jama'a na Shan Azaba

Matsalar Ruwan Sha Ta Yi Katutu a Jihar Gombe, Jama'a na Shan Azaba

  • Al'ummar jihar Gombe na cigaba da fama da karancin ruwan sha duk da gwamnatin jihar na cewa tana kashe miliyoyin Naira domin samar da shi
  • Yankuna da dama a jihar ba su samun ruwan sha daga ruwan da ake samarwa daga ruwan Dadin Kowa da ke karamar hukumar Yamaltu Deba
  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa karancin ruwan ya samo asali daga karuwar jama'a, karin kudin da ake kashewa wajen turo ruwan da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Wani bincike ya nuna ana cewa ci gaba da fama da karancin ruwan sha sakamakon gazawar hukumar ruwa ta jihar Gombe wajen samar da isasshen tsaftataccen ruwa ga mazauna birnin jihar.

Mummunan karancin ruwan ya jefa gidaje mawuyacin hali, inda mazauna ke neman wasu hanyoyin samun ruwa saboda karancinsa.

Kara karanta wannan

Masu POS sun fara barazanar dakatar da aiki a Najeriya

Wani waje da ake diban ruwa a Gombe
Yadda mutane ke bidan ruwa a wani gida a GRA Gombe. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta zagaya sassan birnin Gombe, inda ta gano cewa tsawon watanni, bututun ruwan da ke samar da ruwa ga wasu unguwanni da ke da alaka da babban matatar ruwan jihar duk suna bushe.

Wannan ya tilasta wa mazauna da dama dogaro da rijiyoyin burtsatse masu zaman kansu a matsayin mafita, amma hakan na zuwa ne da tsada, wacce a mafi yawan lokuta take da yawa ga talaka.

Wadanda ba za su iya biyan kudin ba kuwa suna shafe sa’o’i suna layi a rijiyoyin da ke sayar da ruwa da rahusa ko kuma suke bayar da shi kyauta a matsayin taimako.

Wuraren da ake wahalar ruwa

Unguwannin da suka fi fama da matsalar sun hada da Tudun Wada, Bolari, Pantami, Herwagana, Kumbiya-Kumbiya da wasu sassan Jekadafari.

A Tudun Wada, rahoton ya gano cewa babu ruwan sha daga hukumar ruwa ta jihar tsawon watanni, yayin da ko a wasu yankunan Jekadafari ma ruwa ba ya zuwa a kai-a kai.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bukaci Tinubu ya dawo da mafi karancin albashi N100,000

Haka a unguwanni irin su GRA, New GRA, Federal Low Cost, Buba Shongo, Shongo Estate, Orji Estate da Abuja Quarters na fama da matsalar, inda ake ganin galibin mazaunan masu hannu da shuni ne da ’yan siyasa ke dogaro da motocin dakon ruwa.

Matsalar ta fi shafar unguwanni kamar Arawa, Kagarawal, Riyal, Bomala, Nayi Nawa da Tumfure, saboda yawancinsu ba su da alaka da tsarin samar da ruwan Dadin-Kowa.

Wajen da ake bidan ruwa a Gombe
Yara sun fito divan ruwa a cikin unguwar GRA Gombe. Hoto: Legit
Source: Original

Farashin ruwa a jihar Gombe

Mutane da dama sun ce ruwa ya yi tsada sosai, musamman a lokacin rani. Jarkar ruwa 10 na iya kai wa N1,000 ko fiye, gwargwadon wurin da mutum yake da kuma yawan rijiyoyin kasuwanci da ke yankin.

Wani malamin makarantar sakandare da ke zaune a Bolari, Abubakar Musa ya ce yana kashe N600 a kullum wajen sayen ruwa.

Ya ce:

“A unguwarmu, jarka 10 na ruwa na kai N600 idan akwai wutar lantarki, amma idan suna amfani da janareta sai ya kai tsakanin N800 zuwa N1,000.
"Ina kashe sama da N18,000 a wata kan ruwa kadai. A matsayina na sabon wanda ya kammala karatu kuma malami, albashina bai kai N80,000 ba a wata, sannan ina ciyar da mutum uku a kullum. Ka ga irin wahalar da muke ciki.”

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya hurawa Tinubu wuta, yana so ya sauka daga mulkin Najeriya

Hakazalika wani ma’aikacin gwamnati, Malam Abubakar Haruna ya ce samar da ruwan amfanin gida ga iyalinsa ya zama kalubale sosai.

“Ni karamin ma’aikaci ne kuma albashina ba ya kai ni ko’ina. Albashina yana karewa kafin tsakiyar wata. Wannan shi ne shekara ta biyar da nake zaune a Arawa amma bututun ruwa bai taba kawowa ko rana guda ba.
"Muna dogaro dari bisa dari da rijiyoyin burtsatse masu zaman kansu kuma suna karbar N600 ko fiye ga jarka 10."

A Federal Low Cost, GRA da Tumfure, wadanda ake dauka a matsayin manyan unguwanni, mazauna na amfani da motocin dakon ruwa masu zaman kansu domin cika tankunansu na sama, inda kudin hakan ke kai wa N9,000 ko fiye.

Wani mazaunin Tumfure, Joseph David, ya ce yana kashe har N50,000 a wata kan ruwa saboda yankin ba shi da alaka da bututun ruwa.

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe a wajen taron siyasa. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: UGC

Legit ta tattauna da Malam Ahmad

A tattauna da wani dan kasuwa da ke zaune a Pantami ta Yamma, Malam Ahmad Adamu ya bayyanawa Legit Hausa cewa suna fama da matsalar ruwa sha sosai.

Kara karanta wannan

Babbar salla: Tinubu ya saukaka wa yan kasa, ya rage kudin sufurin jiragen kasa

"Jarka 10 suna kai wa N700 zuwa N1000. Idan muna son samun sauki sai dai mu dauki hayan kuskus mu ba yaran mu su je su debo a burtsatse. Hakan kuma zai iya hana su zuwa makaranta."
"A kwanakin baya sai da yarona ya karye a hannu duk a masifar debo ruwa."

Martanin Gwamnatin Gombe

Shugaban hukumar ruwa ta jihar Gombe, Abubakar Sadiq Muhammed ya ce matsalar samar da ruwa a jihar ta samo asali ne daga haduwar matsalolin gudanarwa, abubuwan more rayuwa, karuwar jama’a da kuma wasu dalilai.

A cewarsa, duk da cewa jarin da gwamnati ta zuba ya nuna kudirinta na tabbatar da samar da tsaftataccen ruwa, akwai kalubale da dama da ke ci gaba da shafar inganci da dorewar samar da ruwan.

“Daya daga cikin manyan kalubalen samar da ruwa mai dorewa shi ne tsadar makamashin da ake bukata wajen gudanar da matatar ruwa ta Dadin-Kowa.
"Wani babban bangare na kudin da ake warewa a kowane wata yana tafiya ne wajen biyan kudin wutar lantarki da sinadaran da ake amfani da su wajen tace ruwa domin tura shi da rarraba shi a fadin birnin akalla sau biyu a mako,”

Kara karanta wannan

Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki

In ji shi

Duk da matsalar da ake fama da ita, Aminiya ta rahoto cewa gwamna Inuwa Yahaya ya ce suna kashe N150m duk wata domin samar da ruwa a fadin jihar Gombe.

Gombe ta hada kai da kasar Tunisia

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin jihar Gombe ta hada kai da wasu kamfanonin kasar Tunisia domin inganta abubuwan more rayuwa.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar za ta hada kai da kamfanonin ne domin inganta samar da ruwan sha, samar da ayyuka da sauransu.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da wata tawaga mai karfi sun gana da 'yan Tunisia a watan Fabrairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng