Masu POS Sun Fara Barazanar Dakatar da Aiki a Najeriya

Masu POS Sun Fara Barazanar Dakatar da Aiki a Najeriya

  • Kungiyar masu POS ta ce za ta iya dakatar da ayyukanta a fadin kasar nan saboda wasu matsaloli da ta dade tana fuskanta a Najeriya
  • Ta ce za ta daina aiki ne idan CBN da hukumar FCCPC ba su shiga tsakaninta da kamfanonin Verve International da Interswitch Limited ba
  • Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba ta shawara kan harkokin yada labarai, Yomi Idowu, ya sanya wa hannu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar masu POS ta ce za ta iya dakatar da ayyukanta tare da kawo cikas ga harkokin banki a fadin Najeriya.

Ta yi barazana ne tana mai cewa za ta dauki matakin idan bankin CBN da FCCPC ba su gaggauta shiga tsakani kan wani tsarin da ake zargin wasu kamfanoni biyu suna aiwatarwa ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Trump zai kawo sabon kudi mai dauke da hoton shi a Amurka

Mai POS na kirga kudi
Yadda wani mai POS ke kirga kudi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba ta shawara kan harkokin sadarwa, Yomi Idowu ya sanya wa hannu.

Korafin masu POS a Najeriya

A cewar Idowu, masu POS sun rubuta takardar korafi kan abin da suka kira ci gaba da daukar matakai ba bisa ka’ida ba daga kamfanonin biyu, Verve International da Interswitch Limited

Idowu ya ce ayyukansu sun saba wa dokoki da ka’idojin da babban bankin Najeriya da dokar kare samar da kayayyaki da ayyukan yau da kullum ta shekarar 2018 suka tanada.

Ya ce a matsayinsu na wakilan hadakar kamfanonin da ke da lasisin CBN kan harkokin kudi, ba za su samu wani zabi ba face dakatar da karba, sarrafawa da gudanar da hada-hadar katin Verve.

An nakalto kungiyar tana cewa:

“Wannan mataki ya zama dole saboda ci gaba da karuwar ayyukan da ba su dace da doka ba daga wadannan kamfanoni, wadanda tare suke tauye ka'idar tsarin biyan kudi na Najeriya, suna rage jarin cibiyoyin da abin ya shafa, tare da karya dokoki da dama na hukumomi.”

Kara karanta wannan

Ana tsoron bullar cutar Ebola mai hadari a Kano, Borno da wasu jihohin Najeriya

Wajen da ake cire kudi ta POS
Wasu mutane suna cire kudi a wajen masu POS. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Zargin da masu POS ke yi

Jaridar This Day ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana cewa laifuffukan da take zargin kamfanonin da aikatawa sun hada da:

a) Ci gaba da rike cikakken iko kan sarrafa hada-hadar katin Verve

b) Nuna fifiko a kasuwar katin ta hanyar da ta saba wa Sashe na 72 na dokar kare masu amfani da kayayyaki ta 2018 da kuma sashe na 3, 4 da 7.3 na ka’idojin babban bankin Najeriya kan hanyoyin biyan kudi ta yanar gizo

c) Cire kudi daga asusun masu karbar kudi da masu hada-hadar kudi ba tare da izini ko bisa ka’ida ba

An kara kudin katin ATM

A wani labarin, mun kawo muku cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya yi karin kudin mallakar katin cire kudi na ATM a fadin kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa bankin ya kara kudin da kashi 50 cikin 100, inda a yanzu za a rika biyan N1,500 kafin mallakar katin.

A daya bangaren kuma, bankin CBN ya kara da cewa ya soke kudin kula da katin ATM da bankuna ke cirewa a asusun abokan hulda a kowane wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng