Ana fama da wahalar ruwan sha a Sokoto a lokacin rani
- Ruwa ya zama wani kayan gabas a wannan lokaci a Garin Sokoto
- ‘Yan Ga-ruwa shar don kuwa abubuwa ta gyaru masu a halin yanzu
- Ana ganin sauyin yanayi musamman a wannan lokaci ma na rani
Labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust cewa wahalar ruwan sha ya tasa jama’a a gaba a Jihar Sokoto inda yanzu sai bayin Allah sun yi doguwar tafiya kafin su samu abin da za su yi aiki da shi.
Rahoto ya zo mana cewa mutane su kan yi tafiya ta tsawon kilomita da dama domin samun ruwan da za su yi amfani da shi a gida. Masu ruwa dai shar a wajen su yanzu inda ake saida gorar ruwa har kan N50 a maimakon N20.
KU KARANTA: 'Yan Sandan da ke gadin Shugaban kasa sun yi zanga-zanga
Mutanen Gari sun koka da yadda su ke sayan ruwa har a kan N500 a rana. Masu hali kuwa na sayen tankin ruwa ne na lita 10, 000 a kan N6, 000. Wasu masu abin hannun kuwa su kan gina rijiyar burtsatsi na zamani a Garin.
Kwamishinan harkokin ruwa na Jihar Muhammad Arzika Tureta ya bayyana cewa ruwan dam din Goronyo ne yayi kasa wanda shi ke ba Jihar ruwa. Yanzu dai an fara ganin sauyin yanayi ne a kusan Duniyar baki daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng