Babbar Salla: Tinubu Ya Saukaka wa Yan Kasa, Ya Rage Kudin Sufurin Jiragen Kasa
- Gwamnatin tarayya ta amince da rage kudin tikitin jirgin kasa domin saukaka wa ‘yan Najeriya tafiye-tafiyen bikin babbar salla
- Ma’aikatar sufuri ta bayyana cewa rangwamen zai fara aiki daga ranar 26 ga Mayu zuwa 1 ga Yuni, yayin da jadawalin jiragen kasa ba zai canza ba
- Fasinjojin da suka sayi tikiti kafin sanarwar gwamnati za su samu rabin kudinsu a matsayin rangwame domin sake amfani da shi kafin ranar 1 ga Yuni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da rage kudin tikitin dukkan jiragen kasa na fasinja da kashi 50 a kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin ta dauki matakin ne saboda bikin babbar salla na shekarar 2026 domin taimaka wa matafiya.

Source: Twitter
Ma’aikatar sufuri ta kasa ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da babban sakatare, Injiniya Funsho Adebiyi ya sanya wa, cewar Punch.
Babbar salla: An rage farashin jigilar jiragen kasa
Sanarwar ta ce rangwamen zai fara aiki daga ranar 26 ga watan Mayu zuwa ranar 1 ga watan Yuni domin rage wa ‘yan Najeriya nauyin kudin sufuri.
Ma’aikatar ta kara da cewa dukkan hanyoyin jirgin kasa na NRC a fadin Najeriya za su yi aiki da sabon farashin da aka rage da rabinsa.
Haka kuma, wadanda suka sayi tikiti kafin sanarwar gwamnati za su samu dawo da rabin kudinsu domin sake amfani da shi kafin ranar 1 ga Yuni.

Source: Facebook
Yadda jadawalin zirga-zirgar zai kasance
Gwamnati ta tabbatar da cewa jadawalin tashi da zirga-zirgar jiragen kasa ba zai samu wani sauyi ba yayin gudanar da bikin babbar salla a Najeriya.
Ma’aikatar sufuri ta gode wa ‘yan Najeriya bisa ci gaba da bai wa gwamnati hadin kai tare da yi wa Musulmai fatan gudanar da Sallah cikin kwanciyar hankali.
Sanarwar ta ce:
“Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya tana godiya da ci gaba da goyon bayan da ‘yan Najeriya suke bai wa gwamnati, tare da yi wa dukkan fasinjoji da al’ummar Musulmi fatan gudanar da bikin babbar salla cikin zaman lafiya da farin ciki. Barka da Sallah.”
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa hukumar NRC na gudanar da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyoyin Lagos zuwa Ibadan da Abuja zuwa Kaduna da Warri zuwa Itakpe.
Kamfanin jirgin kasan kuma yana gudanar da layukan dogo masu matsattsun hanya a jihohin Lagos da Ogun domin saukaka zirga-zirgar matafiya a yankunan.
Gwamnatin Tinubu za ta inganta sufurin jiragen kasa
A wani labarin, an ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana shirin kaddamar da sabuwar taswira domin hada jihohi 36 da Abuja da titin layin dogo.
Shugaban hukumar jiragen kasa, Kayode Opeifa, ne ya bayyana hakan a taron sufuri na kasa karo na bakwai da aka yi inda ya fadi muhimmancin shirin ga kasar bai daya.
Ya ce shirin na da alaka da manufar 'Renewed Hope' ta shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta bunkasa tattalin arziki da kuma inganta walwalar jama'ar kasa.
Asali: Legit.ng

