Rashin Tsaro: Atiku Ya Hurawa Tinubu Wuta, Yana So Ya Sauka daga Mulkin Najeriya
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gaza matuka wajen magance matsalar tsaro
- Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki domin tabbatar da kubutar da daliban makaranta da aka sace a jihohin Oyo da Borno
- Yayin da ya yi kira ga Tinubu ya sauka, Atiku ya nuna damuwa kan tabarbarewar matsalar tsaro a kasar, yana mai cewa hakan na barazana ga ilimi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda ‘yan ta’adda ke ci gaba da barazana ga jama’a ba tare da hukuma ta dauki matakin da ya dace ba.
Atiku Abubakar ya yi magana ne yayin da 'yan ta'adda ke cigaba da kai hare-hare da sace mutane a jihohi daban-daban a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan
Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Source: Getty Images
Atiku ya nemi Tinubu ya sauka
Yayin da yake cewa babban nauyin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da jin dadin jama’arta, Tribune ta ce Atiku ya bukaci shugaba Tinubu da ya sauka daga mulkin kasar.
“Shugaba Tinubu ba shi da wani dalili da zai sa ya ci gaba da zama a Aso Rock ko da kwana guda idan daruruwan ‘yan kasa da aka sace na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.
“Wace irin gwamnati ce za ta bari wasu kungiyoyi da ba na gwamnati ba su mayar da kasar zuwa filin kashe-kashe da kuma mafakar masu garkuwa da mutane da karbar kudin fansa?”
In ji Waziri Adamawa a cikin wata sanarwa da ofishin yada labarai na Atiku ya sanya wa hannu ranar Alhamis, 28 ga watan Mayun 2026.
Maganar sace dalibai a Oyo
'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki domin kubutar da daliban makaranta da aka sace a jihohin Oyo da Borno cikin koshin lafiya.
Akalla dalibai 42 aka sace ranar 15 ga Mayun 2026 yayin hare-haren ‘yan ta’adda a karamar hukumar Askira-Uba ta jihar Borno.
A wannan rana kuma, an sace dalibai da malamai sama da 40 daga wata makaranta a jihar Oyo. An kuma ruwaito cewa an sare kan wani malami.

Source: Facebook
Business Day ta wallafa cewa Atiku ya ce yin Allah-wadai kawai da sace-sacen ‘yan ta’adda ba zai wadatar ba idan ba a bi shi da kokarin ceto wadanda aka sace cikin gaggawa ba.
An fatattaki mutane a Katsina
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Amnesty International ta fitar da sanarwar cewa 'yan ta'adda na cigaba da fatattakar mutane a Sokoto.
Amnesty ta ce a yanzu haka dubban mutane sun koma 'yan gudun hijira a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni saboda hare-haren 'yan bindiga.
Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara kaimi wajen ceto al'ummar kasar da suka shiga damuwa da matsaloli saboda rashin tsaro.
Asali: Legit.ng
