Za’a yi wa Gwanatin Kano karo-karo don ta magance matsalar Ruwan sha a jihar
- Jihar na daya daga cikin jahohin dake fama da kamfar Ruwan sha a jihar duk kuwa da cewa Gwamnatin jihar na kashe makudan kudi wajen samar da Ruwan sha ga jama'ar jihar, amma wannan baya rasa nasaba da kara yawa da jama'ar jihar keyi a kullum ga kuma baki da suke tururuwar shiga jihar a kullum
Kwamishinan Ruwa na jihar Kano Alhaji Usman Riruwai ya gabatar da wani tsari da za’a shafe kimanin shekara biyar da ana aiwatar da shi domin maganace matsalar Ruwan sha a cikin kwaryar birnin Kanon. Tsarin da zai lakume makudan biliyoyin Naira da ya kai N98b.
An dai gabatar da wannan tsari ne yayin gudanar da taron tattaunawa da juna domin lalubo hanyoyin ciban jihar a wani bangare na bikin ranar Dimukuradiyya da Gwamnatin jihar ta shirya a jiya Talata.
KU KARANTA: Kotu ta yankewa tsohon gwamna Nyame hukunci shekaru 11 bayan gurfanar da shi
Alhaji Usman Riruwai ya bayyana cewa wannan tsari da jihar ta bullo da shi zai samu tallafi ne daga wasu masu bayar da agaji daga kasashen ketare tare da Gwamnatin tarayya.
Riruwai ya ce Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje zata bayar da N25b sai kuma Bankin cigaba na Musulunci zai tallafa da N45b yayin da Hukumar cigaba na kasar Faransa zai tallafa da N27b sai kuma kungiyar tarayyar Turai zata bayar da gudummawar N21b.
Ragowar wadanda zasu tallafa sun hada da; UNICEF N1.5b sai DFID N1b a karshe kuma Gwamnatin Tarayya zata bayar da N3.5b domin ganin aikin ya samu nasara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng