Tinubu: "Yadda Muka Ceto Najeriya daga Rugujewa a Shekaru 3 na Mulkina"
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa ta ɗauki matakai masu wahala domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga durƙushewa
- Ya bayyana cewa an samu ci gaba a fannoni kamar hanyoyi, ilimi, noma, gidaje da makamashi cikin shekaru uku da ya yi a karagar mulkin kasar nan
- Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sadaukarwar da suka yi ba ta tafi a banza ba domin ƙasar na dawowa cikin hayyacinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ce matakan gyaran tattalin arzikin da gwamnatinsa ta ɗauka cikin shekaru uku da suka gabata sun taimaka wajen ceto Najeriya daga faɗawa cikin mummunan rikicin tattalin arziki.
Tinubu ya bayyana haka ne a cikin jawabin cikar shekaru uku na gwamnatinsa ranar 29 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan
Ayyukan da Tinubu ya saka a gaba bayan gwamnatinsa ta shekara 3 a mulkin Najeriya

Source: Facebook
A cikin sanarwar da hadiminsa Bayo Onanuga ya wallafa a shafn X, Tinubu ya ce duk da wahalhalun da jama’a suka fuskanta, yanzu ana fara ganin alamun ci gaba a fannoni daban-daban.
Tinubu ya fadi yadda ya samu Najeriya
Shugaban ya ce lokacin da ya hau mulki a shekarar 2023, Najeriya na fama da matsaloli masu yawa da suka haɗa da tallafin mai da ya zama nauyi ga gwamnati, ƙarancin kuɗin shiga, matsalar canjin kuɗi, hauhawar bashin gwamnati da matsalar tsaro.
A cewarsa, a lokacin tsarin tallafin mai, Najeriya na kashe kusan N18.4bn a kullum wajen tallafin fetur, yayin da aka kashe sama da N4tr a shekarar 2022 kaɗai.
Ya ƙara da cewa tsarin canjin kuɗi iri-iri da harkar anfani da bambamcin farashin Dala sun jawo asarar sama da N8tn cikin shekaru uku.
Tinubu ya yi bayanin ci gaban tattalin arziki
Shugaban ƙasar ya ce gwamnati ta ɗauki matakai masu wahala amma masu muhimmanci domin hana ƙasar shiga matsanancin rikici.
Tinubu ya ce:
“Da mun ƙi ɗaukar matakai, Najeriya za ta fada cikin matsalar durƙushewar kuɗI, talauci da rashin tabbas a tattalin arziki.”
Ya bayyana cewa yanzu tattalin arzikin Najeriya ya fi ƙarfi idan aka kwatanta da shekarar 2023, yayin da kasuwar hannayen jari ta samu bunƙasa daga darajar N30tn zuwa N160tn a shekarar 2026.
Shugaban ya ce ana gudanar da manyan ayyukan hanyoyi sama da kilomita 2,700 a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da hanyar Legas zuwa Calabar, Sakkwato zuwa Badagry da Abuja zuwa Kano.
A bangaren man fetur da iskar gas kuwa, Tinubu ya ce sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo sun jawo sababbin jarin biliyoyin daloli daga kamfanonin ƙasa da ƙasa.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana cewa gwamnati ta tallafa wa miliyoyin manoma ta hanyar samar da iri, taki, injina da hanyoyin ban ruwa.
Ya ce Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya ya bai wa ɗalibai sama da miliyan 1.5 damar samun ilimi mai zurfi, inda aka raba sama da N282bn.
Haka kuma ya ce shirin gidaje na Renewed Hope ya samar da gidaje sama da 10,000 a jihohi 14 da Abuja, tare da samar da ayyukan yi fiye da 300,000.
Ya shawarci yan Najeriya su ci gaba da bayar da hadin kai domin a kai ga cika burin da aka saka a gaba na samun ci gaba mai dorewa a kasar.
Tinubu ya karyata zargin barin Musulunci
A baya, mun kawo labarin cewa Fadar Shugaban kasa ta ce jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi ridda, ya bar addinin musulunci ba gaskiya ba ne.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa har yanzu Bola Tinubu musulmi ne amma yana mutunta kowane addini domin kowa yana da 'yancin da zai yi addinin da ya ga dama ba tare da takura ba.
Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya bukaci 'yan Najeriya su rika tantance labari kafin fara yadawa a kafafen sada zumunta domin kaucewa fada wa a cikin tarkon labaran karya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

