Bayan Doke Shi a Zabe, Atiku Faɗi Abin da Ya Tattauna da Amaechi a Abuja
- 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya bayyana abin da suka tattauna da Rotimi Amaechi bayan ganawarsu a Abuja
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce sun tattauna matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar Najeriya bayan ya yi nasara a zaben ADC
- Atiku Abubakar ya kuma bukaci Amaechi da Mohammed Hayatu-Deen da suka sha kaye a zabe da su hada kai da shi gabanin zaben 2027 domin a tunakari APC tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana bayanan ganawar da ya yi da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, a gidansa da ke Abuja.
Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, ya ce tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali kan halin da Najeriya ke ciki musamman matsalar tattalin arziki da rashin tsaro.

Source: Facebook
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 29 ga watan Mayu, 2026 Atiku ya bayyana cewa shi da Amaechi sun yi doguwar tattaunawa kan yadda kasar ke fuskantar kalubale masu yawa.
Atiku Abubakar ya ziyarci Rotimi Amaechi
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa shi da Amaechi sun kuma duba rawar da ‘yan Najeriya masu kishin kasa za su taka wajen nemo mafita daga matsalolin da ake ciki.
Ya ce duk da yanayin zumunci da annashuwar da aka yi yayin ganawar, sun yi magana mai zurfi da gaskiya kan tabarbarewar da ake gani a kasar.

Source: Twitter
Atiku ya ce:
“Mun tattauna kan mawuyacin halin da kasa ke ciki, matsin tattalin arziki da ke kara tsananta, rashin tsaro, da kuma nauyin da ke kan ‘yan Najeriya masu kishin kasa na ci gaba da neman hanyoyin ceto kasar daga durkushewa.”
Atiku ya taya Amaechi murna
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa ya taya Amaechi murnar zagayowar ranar haihuwarsa yayin ziyarar.
Ya bayyana Amaechi a matsayin mutum mai hazaka da cikakken kwarewa, inda ya ce sun yi barkwanci kan nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta samu a baya-bayan nan.
Ziyarar ta shi na zuwa ne a lokacin da ADC ke kokarin zama da tsintsiya madaurinki 'daya bayan zaben fitar da gwanin da ya tabbatar da Atiku a matsayin 'dan takarar shugaban kasa a 2027.
Shawarar Atiku ga Tinubu
A baya, kun ji cewa 'dan takarar shugaban kasa a zaɓe mai zuwa, Atiku Abubakar ya kalubalanci Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin babban zaɓen 2027 da za a yi a Najeriya.
Wanda ya samu tikitin ADC ya ce ya kamata shugaban kasa, Bola Tinubu ya tattara kayansa ya koma Legas domin za a kawo karshen wa'adinsa bayan 'yan Najeriya sun kada kuri'arsu.
Atiku ya lashe zaɓen fitar da gwani na ADC da ƙuri’a sama da miliyan 1.8 a shirin da 'yan adawa ke yi na tunkarar babban zaɓe mai zuwa da kuma fatan za su yi nasara a kan Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

