2026: Muhimman Abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

2026: Muhimman Abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ta fara ganin haske bayan gyaran tattalin arziki da gwamnatinsa ta yi a shekaru uku
  • Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a sakon taya Musulmi murnar zagayowar bikin Babbar Sallah, inda ya yi kira da a hada kai da kaunar juna
  • Shugaban kasar ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da murƙushe ‘yan ta’adda domin samar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi a Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar Babbar Sallah.

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su rungumi sadaukarwa, haɗin kai da tausayi kamar yadda Annabi Ibrahim (AS) ya koyar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu yan aika sakon barka da Sallah ga 'yan Najeriya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya na rattaba hannu kan wasu takardu a Eagle Square, Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Wannan na kunshe ne a cikin saƙon barka da Sallah da fadar shugaban ƙasa ta fitar ranar Talata, ta hannun mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Atiku vs Amaechi: ADC ta sanar da sakamakon zaben fitar da 'dan takarar shugaban kasa a Kano

Tinubu ya aika sakon barka da Sallah

Tinubu ya ce bikin 'Eid-el-Kabir' na tuna wa mutane muhimmancin biyayya ga Allah da kuma sadaukarwa domin kyakkyawar manufa.

A cikin sakon, Tinubu ya ce:

“Mun gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya raya mu muka sake shaida wannan babban biki na babbar sallah.”

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatinsa ta aiwatar suna da wahala, amma sun zama dole domin gina Najeriya mai ƙarfi da ci gaba.

Ya ce:

“Kamar yadda sadaukarwa ke haifar da lada, ina farin cikin cewa sadaukarwa da ƙoƙarin da muka yi cikin shekaru uku da suka gabata sun samar da tattalin arziki mai ɗorewa, wanda ya sa Najeriya ta zama wurin zuba jari.
“Mun ratsa ta cikin duhun rami, amma a karshensa haske ya bayyana.”

Tinubu ya yi magana kan tsaro

Shugaban ƙasar ya amince cewa har yanzu akwai hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a wasu yankuna duk da ƙoƙarin jami’an tsaro.

Kara karanta wannan

Sakon uwargidan Tinubu ga al'ummar Musulmi yayin da ake shirin babbar salla

Sai dai ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen murƙushe miyagu.

Tinubu ya ce: “

Ina tabbatar muku cewa ba a manta da ku ba kuma ba a yashe ku ba. A ƙarshe za mu yi nasara a kan dukkan 'yan ta'adda.”

Ya kuma yi kira ga Musulmi su yi addu’a domin zaman lafiya da karfin hikimar mulki ga shugabanni, tare da taimaka wa marasa galihu a lokacin bikin Sallah.

Sugaba Bola Tinubu ya bukaci Musulmin Najeriya su dage da yiwa kasa hidima a yayin babbar sallah.
Shugaba Bola Tinubu da wasu kusoshin gwamnati a wajen sallar idi. Hoto: @Dolusegun16
Source: Twitter

Gwamnati za ta ci gaba da ayyukan raya ƙasa

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da saka hannun jari a fannoni kamar tsaro, noma, gine-gine da bunƙasa rayuwar jama’a.

Ya ƙara da cewa:

“Gwamnatina na da ƙudurin gina Najeriya inda kowa zai rayu cikin zaman lafiya, ya yi addininsa cikin ‘yanci kuma ya cimma burinsa ba tare da tsoro ba.”

Tinubu ya kammala da yi wa ‘yan Najeriya fatan Sallah lafiya da albarka, yana addu’ar Allah ya karɓi ibadu da sadaukarwar al’umma.

An ba ma'aikata hutun babbar sallah

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Tinubu ya cancanci 'yan Najeriya su kara ba shi dama a zaben 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Najeriya ta ba da hutun kwanaki biyu ga ma'aikata domin su samu damar gudanar da shagulgulan babbar Sallah ta bana 2026.

Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Oji ya taya daukacin musulmi murnar zagayowar babbar sallah, daya daga cikin ibadun addinin musulunci.

Gwamnatin tarayya ta kuma buƙaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a da nazari domin neman shiriyar Allah ga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com