Da Gaske Shugaba Tinubu Ya Yi Ridda, Ya Fita daga Addinin Musulunci? Gaskiya Ta Fito

Da Gaske Shugaba Tinubu Ya Yi Ridda, Ya Fita daga Addinin Musulunci? Gaskiya Ta Fito

  • Jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi ridda, ya bar addinin musulunci ba gaskiya ba ne
  • Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa har yanzu Bola Tinubu musulmi ne amma yana mutunta kowane addini
  • Hadimin shugaban kasa, Dada Olusegun ya bukaci 'yan Najeriya su rika tantance labari kafin fara yadawa a kafafen sada zumunta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wasu rahotanni da faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bar addinin Musulunci.

Hadimin shugaban kasa kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun, ya fito ya musanta rade-radin cewa Shugaba Tinubu, ya sauya addini.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da wasu manyan jami'an gwamnati a masallaci Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Olusegun ya fadi hakan ne wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da wani bidiyo da ake yadawa wanda ke ikirarin cewa shugaban ya sauya addini.

Kara karanta wannan

2026: Muhimman abubuwa da Tinubu Ya Fadawa 'Yan Najeriya a Sakon Barka da Sallah

Shin Tinubu Musulmi ne har yanzu?

A cewar hadimin shugaban, babu wani sauyi da aka samu a addinin shugaban kasa, yana mai jaddada cewa Tinubu Musulmi ne kuma har yanzu yana ci gaba da gudanar da addininsa cikin tsari da biyayya.

Ya bayyana rade-radin da ake yadawa a matsayin karya marar tushe, yana mai cewa wasu mutane ne ke kokarin amfani da kafafen sada zumunta wajen yaudarar jama’a da haddasa rudani a tsakanin al’umma.

“Shugaban kasa bai sauya addininsa ba. Ya kasance Musulmi kuma har yanzu yana gudanar da addininsa kamar yadda ya saba,” in ji Olusegun.

Ya yi magana kan addinin matar Tinubu

Dada Olusegun ya kuma yi karin haske kan yadda shugaban kasa ke mutunta bambancin addini a cikin gidansa, musamman ganin cewa mai dakinsa, Sanata Oluremi Tinubu, Kirista ce kuma fasto.

A cewarsa, dangantakar da ke tsakanin Tinubu da matarsa alama ce ta zaman lafiya, hakuri da fahimtar juna tsakanin mabambantan addinai, abin da ya kamata ‘yan Najeriya su yi koyi da shi.

Kara karanta wannan

Sheikh Aminu Daurawa ya jero darusa 10 ga kowane Musulmi a ranar Arafa

Bidiyon da ya haddasa ce-ce-ku-ce

Rahotanni sun nuna cewa ce-ce-ku-cen ya fara ne bayan wani bidiyo ya bayyana a kafafen sada zumunta inda wasu mutane suka yi ikirarin cewa shugaban kasa ya rungumi Kiristanci.

Bidiyon ya jawo martani daban-daban daga masu anfani da shafukan sada zumunta, inda wasu suka nuna mamaki yayin da wasu suka fara yada bayanan ba tare da tantance gaskiyarsu ba.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana ganawa da wata tawaga a fadar Aso Rock Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Sai dai Olusegun ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirari, yana mai cewa ana yada irin wadannan bayanai ne domin tayar da kura da rikitar da jama’a.

Hadimin shugaban ya yi kira ga jama’a da su rika tantance bayanai kafin yada su, musamman batutuwan da suka shafi addini da shugabanci.

Tinubu ya amince mutane na shan wahala

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da batun cewa talakawa na shan wahalar rayuwa a karkashin mulkinsa

Bola Ahmed ya yi ikirarin rasa barci saboda tarin matsalolin da suka shigewa yan kasar nan a gaba, wanda hakan ya jawo shi ma ya rame.

Kalaman shugaban kasar na zuwa ne yayin da hasashe ke nuna cewa miliyoyin yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa zakamakon tsare-tsaren tattalin arziki na Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262