Wike Zai Rusa 'Ruga' da Aka Samar Babu Ka’ida a Abuja, Ya Fadi Illarsu ga Al’umma

Wike Zai Rusa 'Ruga' da Aka Samar Babu Ka’ida a Abuja, Ya Fadi Illarsu ga Al’umma

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ba da umarnin rusa wasu haramtattun Rugage da ke Kukwaba a birnin Abuja
  • Wike ya bayyana cewa ci gaba da barin matsugunin yana nan zai jefa mazauna Abuja cikin haɗari, saboda masu laifi na buya a wurin
  • Kafin ziyarar wurin, ministan ya duba aikin gina hanyar shiga tashar kashe gobara ta FCT, yana jaddada kudirin gwamnati na inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ba da umarnin rusa wasu haramtattun rugage a wani yankin birnin tarayya, Abuja.

Wike ya bukaci a gaggauta kwashe mazauna tare da rusa wata haramtacciyar unguwa mai suna Ruga da ke gundumar Kukwaba, yana mai cewa wurin ya zama babbar barazana ga tsaron Abuja.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Wike ya umarci rusa wata uguwa a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin da ya ke ba da umarnin rusa maboyar masu laifi. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Wike ya ba da umarnin rusa wata unguwa

An sanar da wannan umarni ne a ranar Juma'a bayan zaman Majalisar Tsaro ta FCT da kuma duba unguwar, wadda ke kusa da Karmajiji, 'yan kilomita kaɗan daga ƙofar shiga birnin Abuja, cewar Punch.

Wike ya ce wannan matsuguni na bukkoki ya zama mafakar masu aikata laifuka, inda suke komawa bayan sun kai hare-hare a sassa daban-daban. Ya yi gargadin cewa ci gaba da barin unguwar zai ƙara jefa rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja cikin haɗari.

Ministan ya bayyana yankin a matsayin mai hatsari yana mai cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, matsalar tsaro za ta iya ƙara muni.

Saboda haka, ya umarci Kwamishinan 'Yan Sandan Abuja da Daraktan Hukumar Kula da Tsare-tsaren Gine-gine su fara nan take rusa gine-ginen da aka yi ba bisa ƙa'ida ba tare da kwashe mazaunan yankin.

Wike ya gano mafakar masu aikata laifuffuka a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike yayin taro a Abuja. Hoto: Lere Olayinka.
Source: Facebook

Alwashin da Wike ya sha game da Abuja

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnatin Tinubu za ta zare tallafin lantarki a 2027

Wike ya sake jaddada cewa Hukumar Gudanarwar FCT ba za ta amince da ci gaba da wanzuwar haramtattun matsugunai da ke zama mafaka ga masu aikata laifuka ba, yana mai cewa gwamnati ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma a babban birnin ƙasa.

Kafin kai ziyarar zuwa unguwar Ruga, ministan ya duba yadda aikin gina hanyar shiga tashar Hukumar Kashe Gobara ta FCT ke gudana a kan titin Arterial SI, cewar Vanguard.

Hanyar tana haɗa Ring Road II da ke gundumar Kaura zuwa titin Oladipo Diya Way a gundumar Gaduwa, wani aiki da ake sa ran zai inganta zirga-zirga da kuma sauƙaƙa ayyukan gaggawa a Abuja.

Wike ya magantu kan yin murabus

Mun ba ku labarin cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ƙalubalanci duk mai musanta nasarorin gwamnatinsa kan titunan ƙauyukan birnin tarayya ya fito cikin sa'o'i 48.

Wike ya ce gwamnatin Abuja ta ba da kwangilar kilomita 317 na tituna, ta kammala kilomita 221, yayin da ake ci gaba da aikin kilomita 96.

Ministan na Abuja ya bayyana cewa zai yi murabus idan aka tabbatar da cewa bayanan da ya bayar ba gaskiya ba ne domin tsira da mutuncinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.