Ayyukan da Tinubu Ya Saka a gaba bayan Gwamnatinsa Ta Shekara 3 a Mulkin Najeriya

Ayyukan da Tinubu Ya Saka a gaba bayan Gwamnatinsa Ta Shekara 3 a Mulkin Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada ci gaba da rage farashin abinci a Najeriya bayan ya yi shekaru uku yana juya akalar kasar
  • Ya bayyana haka ne ta cikin sakonsa na cika shekaru uku a karagar mulki, inda ya ce gwamnati na shirin rage tsadar sufuri nan gaba kadan
  • Shugaban ya yi alkawarin aiwatar da wasu ayyuka da ya ce za su taimaka wa matasan Najeriya wajen rage zaman kashe wando da samar da ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ci gaban ƙasa yana tabbata ne a lokacin da ‘yan ƙasa za su iya gani kuma su taɓa ribar ci gaba a rayuwarsu ta yau da kullum.

Kara karanta wannan

Tinubu: "Yadda muka ceto Najeriya daga rugujewa a shekaru 3 na mulkina"

Ya ce kari a kan ayyukan da gwamnatinsa ke yi a cikin shekaru uku yana mulki, akwai gyaran layin dogo da kuma ƙara zuba jari a fannin makamashi da nufin gina Najeriyar da kowa zai yi alfahari da ita.

Tinubu ya ce zai ci gaba da ayyukan inganta rayuwar yan Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yana magana a Abuja Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A sakon da hadiminsa Bayo Onanuga ya fitar a shafin X, Tinubu ya amince cewa har yanzu ba a magance dukkan matsaloli ba.

Bola Tinubu na son farfado da Najeriya

Sanarwar ta ce shugaban kasa ya kara da cewa duk da Najeriya ba ta kai inda ake so ba, amma ya ce tubalin farfaɗo da tattalin arziki ya riga ya kafu.

A cewarsa, abin da ya rage yanzu shi ne tabbatar da cewa ‘yan ƙasa sun fara jin sauƙin da sauye-sauyen tattalin arziki ke kawowa kai tsaye a rayuwarsu.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da tabbatar da cewa farashin abinci, wanda ya riga ya sauka bayan ya kai kololuwa a shekarun 2023 zuwa 2024, ya ci gaba da sauka.

Ya ce wannan na daga cikin manyan manufofin da gwamnati ta sa a gaba domin rage wahalar rayuwa ga talakawa.

Gwamnatin Tinubu na shirin saukaka sufuri

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Atiku ya hurawa Tinubu wuta, yana so ya sauka daga mulkin Najeriya

Haka kuma ya ce ana aiki wajen rage tsadar sufuri ta hanyar sauya motocin kasuwanci kamar manyan motoci, bas-bas da tasi daga amfani da mai zuwa gas ɗin CNG.

Tinubu ya ce za a mayar da hankali wajen samar wa matasa aikin yi
Shugaba Tinubu a wajen wani taro da ya halarta a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Shugaban kasar ya ce ana ƙara shirin amfani da motocin lantarki. Wannan, a cewarsa, zai taimaka wajen rage farashin sufuri da sauƙaƙa rayuwa a birane da ƙauyuka.

Shugaban ya ƙara da cewa gwamnati na kuma mai da hankali wajen samar da ayyukan yi da inganta damar kasuwanci domin ‘yan ƙasa su samu abin dogaro da kai. Ya ce wannan zai faɗaɗa tattalin arziki da ƙarfafa masana’antu da noma.

Tinubu ya yi kira ga matasa, ma’aikata, ‘yan kasuwa, manoma, jami’an tsaro da ‘yan Najeriya mazauna ƙasashen waje da su ci gaba da ba da gudunmawa wajen gina ƙasa.

Ana son Tinubu ya sauka daga mulki

A baya, kun ji cewa 'dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya gaza matuka wajen magance matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Atiku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki domin tabbatar da kubutar da daliban makaranta da aka sace a jihohin Oyo da Borno a makonnin da suka gabata.

Yayin da ya yi kira ga Tinubu ya sauka, Atiku ya nuna damuwa kan tabarbarewar matsalar tsaro a kasar, yana mai cewa hakan na barazana ga ilimi duk da tsawon lokaci da aka shafe ana kokarin maganin lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng