Trump Ya Hadu da Fushin Iran da Ya Tsokano Tehran kan 'Kwace' Hormuz

Trump Ya Hadu da Fushin Iran da Ya Tsokano Tehran kan 'Kwace' Hormuz

  • Babban jami’in Iran ya mayar da martani ga Donald Trump bayan shugaban Amurka ya yi barazanar ayyana Mashigar Hormuz a matsayin mallakar Amurka
  • Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce Iran ba ta tsoron barazana kuma ba za a iya tsoratar da ita da nuna ƙarfin soji ba.
  • Gharibabadi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin da yake mayar da martani kan kalaman Trump da suka kara dagula rikicin da ke tsakanin Washington da Tehran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran – Iran ta yi watsi da barazanar Donald Trump na ayyana Mashigar Hormuz a matsayin yankin Amurka, tana mai cewa ba za a iya kwace mashigar da saƙon Twitter ko jirgin yaƙi ba.

Gharibabadi ya ce dole ne Amurka ta amince da abin da ya kira gagarumar shan kaye da ta fuskanta a hannun Iran.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Amurka za ta dauki matakin da ba a taba dauka ba a kan Iran

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Donald Trump a hagu da Mojtaba Khamenei a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta yi martani ga Trump

Rahotanni sun nuna cewa Gharibabadi ya yi wa Donald Trump martani ne a wa sako da ya wallafa a shafinsa na X.

Ya rubuta cewa:

“Ba za a iya kwace Mashigar Hormuz da sakon shafin X ba, jirgin dakon jiragen yaƙi, umarni ko jawabi ba.”

Ya ƙara da cewa Iran ba ta tsoron barazana kuma ba za a iya tsoratar da ita ta hanyar nuna ƙarfin soji ba.

A cewarsa, Mashigar Hormuz mallakar Iran ce kuma za ta ci gaba da kasancewa haka, yana mai cewa buɗewa da rufe mashigar zai kasance ne ƙarƙashin umarnin Iran.

Ya ce Iran za ta ci gaba da sanya takunkumi kan zirga-zirgar mashigar har sai Amurka ta amince da abin da ya kira gaskiyar shan kayenta.

Barazanar da Donald Trump ya yi

Martanin jami’in na Iran ya biyo bayan wata sanarwa da Trump ya fitar ranar Alhamis, inda ya ce sojojin ruwan Amurka suna aiwatar da cikakken katanga a mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Amurka ta nuna ba daga kafa, ta caccaki Isra'ila kan taba kawayen Iran a Lebanon

Trump ya kuma ce bayan Amurka ta yaki Iran gaba ɗaya, zai ayyana mashigar Hormuz a matsayin mallakar Amurka nan ba da jimawa ba.

Hasashen masani kan yakin

Wani masanin harkokin siyasa, Paul Musgrave, ya ce kalaman Trump kan ayyana Mashigar Hormuz mallakar Amurka na iya kasancewa ne domin isar da saƙo ga masu zaɓe a Amurka, musamman magoya bayansa.

Al Jazeera ta wallafa cewa Musgrave ya bayyana Trump a matsayin ɗan siyasar da ke amfani da manyan kalamai, yana mai cewa ya kamata a ɗauki wasu kalamansa da muhimmanci amma ba lallai a ɗauke su da gaske ba.

Ya ce Washington ba za ta iya saurin amincewa da shan kaye a hannun Iran ba, kuma ana iya ganin sabon mataki na takunkumin tattalin arziki ko hare-haren yanar gizo.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yana bankwana da jama'a zai shiga jirgi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewarsa, Iran ma ba za ta amince da cewa ta sha kaye ba, lamarin da zai iya sanya yakin ya shiga wani yanayi na “tsayawa cak” a cikin gajeren lokaci zuwa matsakaicin lokaci.

Amurka ta soki kasar Isra’ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani babban jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce ci gaba da kasancewar sojojin Isra’ila a Kudancin Lebanon bai dace da yarjejeniyar tsarin da Amurka ta dauki nauyi ba.

Kara karanta wannan

Trump ya tabbatar da ya sauya jirgin sama a asirce a tafiyarsa saboda tsoron Iran

Jami’in ya bayyana cewa irin wannan mataki na iya kawo cikas ga kokarin samar da zaman lafiya na dogon lokaci a Lebanon.

Ya kuma ce Amurka na sa ran dukkan ɓangarorin za su bi tsarin yarjejeniyar da suka amince da shi, yana mai cewa Isra’ila ta bayyana cewa ba ta da burin mallakar wani yanki na Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng