Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Sarki a Kwara, Sun Sace Mata da Ƴaƴan Mai Martaba

Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Sarki a Kwara, Sun Sace Mata da Ƴaƴan Mai Martaba

  • Fargaba ta mamaye Yashikira bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari fadar sarki tare da sace matansa da wasu daga cikin ‘ya’yansa
  • Rahoto ya nuna cewa 'yan ta'addar sun ƙona wasu sassan fada tare da lalata motoci yayin harin da ya faru cikin dare a jihar Kwara
  • Jami’an tsaro sun fara samame domin ceto waɗanda aka sace bayan rahotannin cewa an dakile yunƙurin kai hari ofishin ‘yan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kwara - Fargaba ta mamaye al’ummar Yashikira da ke ƙaramar hukumar Baruten a jihar Kwara bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari fadar sarki tare da sace mutane da dama.

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Legit.ng cewa akalla mutum biyar aka sace ciki har da matan sarkin da wasu daga cikin 'ya'yansa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki sanatar Abuja, sun tarwatsa taron jam'iyyar ADC

'Yan bindiga sun farmaki fadar mai martaba sarki a Kwara
Sarkin Yashikira, Alhaji Umar Usman da 'yan bindiga suka farmaki fadarsa a Kwara. Hoto: AAMediaCentre, followKWSG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun farmaki fadar sarki

Rahoton jaridar Premium Times kuma ya nuna cewa harin ya faru ne da tsakar dare ranar Litinin 25 ga watan Mayu, 2026.

Wani mazaunin yankin mai suna Nasiru ya ce maharan sun kutsa cikin fadar masarautar Yashikira inda suka banka wa wasu sassan fadar wuta.

Nasiru ya ce:

“Fadar sarkin Yashikira na fuskantar harin 'yan bindiga. ‘Yan ta'adda sun ƙona fada tare da sace mata da yara ciki har da matan sarkin.”

Majiyoyi daga yankin sun ce 'yan ta'addar sun lalata ɗakuna da dama a cikin fadar tare da ƙona motoci a yayin wannan harin.

Sarkin Ilesha Baruba ya jajanta

A wani saƙon jaje da Legit.ng ta samu, Sarkin Ilesha Baruba, Farfesa Halidu Ibrahim Abubakar Sabi Derekureku IV, ya tausaya wa sarkin Yashikira, Alhaji Umar Sariki Usman, Sabi Kpasi II kan harin.

Ya bayyana cewa kai hari fada tamkar kai hari ne ga mutunci da zaman lafiyar al’umma baki ɗaya, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

'Dan gwagwarmaya Sowore ya fito takarar shugaban kasa, zai kara da Tinubu a 2027

“Cikin bakin ciki na samu labarin harin da aka kai fadarka da al’ummar Yashikira. Lallai kai hari a fadar sarki tamkar kai hari ne na mutunci, tarihi, da zaman lafiyar al'ummar da ka ke wakilta."
Jami'an tsaro sun fara samame don ceto mutanen da aka yi garkuwa da su
Taswirar jihar Kwara, inda 'yan bindiga suka sace mata da 'ya'yan sarkin Yashikira. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun dauki mataki

Rahoton Channels TV ya nuna cewa jami'an tsaro sun kaddamar da wani samame na ceto mutanen da aka sace da sanyin safiyar Litinin a fadar sarkin.

An rahoto cewa sojoji da 'yan sanda sun kaddamar da samamen hadin gwiwar a sassa daban daban na yankin domin ceto wadanda aka sace.

Duk da cewa har yanzu 'yan sanda ba su fitar da sanarwa game da harin ba, amma wata majiya ta ce maharan sun so farmakar ofishin 'yan sanda aka dakile su.

'Yan bindiga sun kona fadar sarki

A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga kusan 200 sun kai hari a kauyen Woro dake jihar Kwara inda ake zargin sun hallaka fiye da mutane 35.

Maharan sun banka wa fadar Sarkin Woro wuta tare da shagunan dake kusa yayin da har yanzu ba a san inda sarkin ya shiga ba.

'Yan majalisar yankin sun bukaci gwamnatin tarayya ta tura dakarun soji na musamman domin kakkabe yan bindiga dake addabar Kaiama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com