Boko Haram Ta Shirya Kunar Bakin Wake a Babbar Sallah, Sojoji Sun Dauki Mataki
- Hedikwatar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation Hadin Kai ta bai wa mazauna yankin Arewa Maso Gabas tabbacin ingantaccen tsaro a lokacin babbar sallah
- Rahotanni sun nuna cewa an shirya gudanar da bikin babbar sallah ne a ranar Laraba 28 ga Mayun 2026 bayan hawan Arafa a ranar Talata
- Rundunar sojin ta ce an riga an ɗauki cikakkun matakan tsaro a duk faɗin yankin domin tabbatar da gudanar da bikin cikin lumana duk da barazanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar Operation Hadin Kai ta miƙa sakon taya murna ga dukkan al’ummar Musulmi gabanin bikin babbar sallah na shekarar 1447AH da za a gudanar ranar Laraba, 28 ga Mayu, 2026.
A wata sanarwa da suka fitar, sojojin sun ce suna yi wa dukkan mazauna yankin Arewa Maso Gabas fatan yin bikin cikin lumana da farin ciki.

Source: Twitter
Domin ci gaba da sauke nauyin kare rayuka da dukiyoyi a duk faɗin yankin, rundunar ta sanar a Facebook cewa an riga an tanadi cikakkun matakan tsaro tun kafin lokacin bikin sallah.
Barazanar Boko Haram lokacin bikin sallah
Rundunar ta ce sahihan bayanan sirri da take da su sun nuna yiwuwar wasu ragowar mayaƙan Boko Haram da ISWAP su yi ƙoƙarin amfani da lokacin bikin wajen kai hare-hare kan fararen hula ta hanyar amfani da ‘yan kunar baƙin wake.
Duk da haka, rundunar ta tabbatar wa jama’ar Arewa maso Gabas cewa an yi hasashen waɗannan barazanar tun da wuri kuma an dauki mataki.
Gabanin bikin sallah a ranar Laraba, an tura sojoji zuwa muhimman wurare da wuraren da ake ganin suna cikin haɗari a dukkan sassan yankin ayyukan rundunar.
Baya ga haka, an kunna dukkan kayan sa ido da ISR, an ƙara sintiri, sannan jami’an tsaro suna aiki tare da sauran hukumomin tsaro, CJTF da kungiyoyin sa-kai na al’umma domin hana duk wata barazana da tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan
Sarki Aminu Ado Bayero ya shirya hawan Sallah a Kano, ya aika saƙo ga jami'an tsaro
Kiran sojojin a bikin babbar sallah
Punch ta wallafa cewa rundunar ta ce tana ƙarfafa wa jama’a gwiwa su kiyaye waɗannan shawarwarin tsaro kafin da kuma lokacin bikin:
- A gudanar da sallar Idi da bukukuwa kusa da gidaje da wuraren da aka saba da su gwargwadon iko, kuma a guji manyan tarukan jama'a.
- A kasance cikin taka-tsantsan musamman a wuraren da jama’a ke cunkoso kamar kasuwanni, tashoshin mota, bankuna da filayen sallah.
- A gaggauta kai rahoton duk wani mutum da ake zargi, kayan da aka bari ba tare da kulawa ba, ko wani motsi da ba a saba gani ba zuwa mafi kusa da shingen sojoji, ofishin ‘yan sanda ko cibiyar hulɗa tsakanin jami’an tsaro da fararen hula.
- A bayar da cikakken haɗin kai ga jami’an tsaro yayin sintiri da bincike.
- A guji yawan zirga-zirga ba tare da buƙata ba, musamman da dare ko a wuraren da jami’an tsaro ba su da yawa.
- A guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba ko jita-jitar da za ta iya haifar da firgici a tsakanin jama’a.

Source: Facebook
Sojoji sun fafata da Boko Haram
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun rundunar sojin Najeriya sun fafata da 'yan ta'addan Boko Haram a a wani yanki na jihar Borno.
Bayanan da dakarun Najeriya suka fitar bayan fadan da suka yi sun nuna cewa an gwabza kazamin fada da Boko Haram ne a Kirawa.
Bayan fafatawa da musayar wuta, sojojin Najeriya sun kashe da dama cikin 'yan ta'addan tare da kwato tarin makaman da 'yan Boko Haram ke aiki da su.
Asali: Legit.ng

