Juyin Mulki: Matan Jami’an da ake Zargi Sun Yi Korafi ga Tinubu

Juyin Mulki: Matan Jami’an da ake Zargi Sun Yi Korafi ga Tinubu

  • Matan sojojin da ake tsare saboda zargin suna da hannu a kifar da gwamnati sun roƙi Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da adalci a shari’ar da ake yi masu
  • Sun nuna damuwa kan yiwuwar amfani da tilastawa da azabtarwa wajen karɓar bayanai daga waɗanda ake zargi da kitsa shirin a shekarar 2025
  • Matan sun ce babu wanda ya kamata a yanke wa hukunci ba tare da hujjoji masu inganci da gaskiya da za su tabbatar suna da hannu a shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Matan wasu jami’an sojin Najeriya da ake tsare da su bisa zargin shirya juyin mulki sun roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da gaskiya da adalci a shari’ar da ake yi wa mazajensu.

Kara karanta wannan

"Ni ma na rame": Tinubu ya amince manufofinsa sun jefa ƴan Najeriya a wahala

A wata wasiƙa da suka aikewa shugaban ƙasar ranar Juma’a 22 ga watan Mayu, 2025, matan sun gargadi gwamnati kan hukunta waɗanda ake zargi ba tare da ƙwararan hujjoji ba

Matan sojoji da ake zargi da juyin mulki sun roki Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @iamkennethokonkwo
Source: Getty Images

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa matan, daga ciki har da Shafa’atu Ali Agbo, Fatima Dauda, Josephine Enemona, Nana Aisha, Zara Abba da sauransu, sun yaba wa Tinubu.

Juyin mulki: Matan sojoji sun yabi Tinubu

Politics Nigeria ta kawo rahoton cewa matan sun yaba wa Tinubu bisa amincewa da fara shari’ar, suna masu cewa hakan wani muhimmin mataki ne na tabbatar da gaskiya, fayyace al’amura da neman adalci.

Sai dai sun bayyana fargabar cewa shari’ar na iya fuskantar son zuciya, tilastawa da azabtarwa daga wadanda ke neman bayanai a hannunsu.

A cikin wasiƙar sun ce:

“A matsayinmu na ’yan ƙasa, mun fahimci muhimmancin ladabtarwa a rundunar soji da kuma nauyin da ke kanta wajen kare tsaron ƙasa."
“Haka kuma mun san cewa zarge-zargen tawaye ko shirya juyin mulki manyan laifuffuka ne da bai kamata a ɗauke su da wasa ba."
“Amma saboda girman waɗannan zarge-zarge ne ya sa dole tsarin neman adalci ya kasance cikin gaskiya, adalci da rashin nuna son kai.”

Kara karanta wannan

"Ba za su iya ba," Namadi ya hango nasarar da Shugaba Tinubu zai samu a 2027

Koken matan sojojin da ke tsare

Matan sun tuna da wasu tsofaffin shari’un soja da suka jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda suka ce wasu daga baya sun zama abin nadama a tarihin ƙasar.

Matan sun yi zargin ana azabtar da mazajensu wajen neman bayanai
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen wani taro Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sun ce:

“Daga zarge-zargen juyin mulkin ƙarya zuwa sallamar jami’ai da tsare-tsaren da aka yi masu na tsawon lokaci, ’yan Najeriya sun sha ganin lokutan da shari’a ta rikide zuwa tsanantawa.”

Sun kuma nuna damuwa kan tsare jami’an na dogon lokaci da kuma rahotannin azabtar da wadanda ake zargi da ake zargin an yi masu.

A cewarsu, akwai rahotannin da ke nuna cewa wasu bayanan furuci an samu su ne ta hanyar matsin lamba da tilastawa, sabod ahaka sun nemi gwamnati ta sa ido domin a tabbatar da adalci.

Ma'aikaci ya yi fallasa kan shirin juyin mulki

A baya mun ruwaito cewa wani ma’aikacin fadar shugaban ƙasa ya bayyana rawar da ya fara taka wa a shirin juyin mulki da aka so kitsa wa domin hambarar da Gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Benue: Ƴan bindiga sun yi yunkurin kai hari a wurin zaben fitar da gwani na APC

Wanda ake zargi Zekeri Umoru ya tabbatar wa da kotu cewa shi ne wanda aka nema da ya tara sojoji da jami’an DSS domin shirin juyin mulkin har cikin Aso Villa da shirya yadda za a shiga ciki.

Ya yi bayani dalla-dalla a kan shirin da aka fara yi wajen kashe wutar lantarkin Aso Rock Villa domin sauƙaƙa aiwatar da shirin bayan ya shiga da sojojin a boye ta cikin wata motar daukan mara lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng