Sojoji Sun Yi wa Boko Haram Ruwan Bama Bamai ana Shirin Sallah
- Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta ce hare-haren saman da ta kai sun kashe mayakan Boko Haram da dama tare da lalata muhimman sansanonin su
- Kakakin rundunar, Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Laraba, yana mai cewa sun kai hari kan maboyar ‘yan tada kayar baya
- A cewar Ehimen Ejodame, an gudanar da hare-haren ne ranar Talata, 26 ga Mayu, bayan samun sahihan bayanan leken asiri da sa ido daga sama (ISR)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin saman Najeriya ta ce dakarun da ke yaki da ta’addanci a jihar Borno sun kai hari kan maboyar ‘yan ta’adda da wuraren ajiyar kayayyakin aiki a Biramiri da ke yankin Gezuwa na jihar.
Hakan na zuwa ne yayin da rundunar sojin ta ce ta shirya tsaf wajen yaki da duk wata barazana da 'yan ta'addan za su haifar musamman a lokacin bikin babbar sallah.

Kara karanta wannan
Bayan 'yan ta'adda sun kutsa makaranta an sace dalibai, gwamna Zulum ya dauki mataki

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa an fadi haka ne a wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na hedikwatar rundunar sojin sama, Ehimen Ejodame, ya fitar ranar Talata.
Barnar da aka yi wa Boko Haram
Ejodame ya ce hare-haren na musamman da aka tsara sun lalata muhimman sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe mayaka da dama da ke aiki a yankin.
Yayin da ya ke cewa an gudanar da aikin ne bayan samun sahihan bayanan leken asiri da sa ido, Ejodame ya ce:
“Wadannan hare-hare da aka tsara sun lalata muhimman sansanonin ‘yan ta’adda tare da kashe mayaka da dama, lamarin da ya kara raunana karfin ayyukan ‘yan tada kayar bayan,”
Ya kara da cewa hare-haren saman da ake ci gaba da kai wa sun haddasa tsoro da rudani tsakanin ‘yan ta’adda a yankin Sambisa.

Source: Facebook
Boko Haram sun firgita a daji
A cewar Ejodame, bayanan leken asiri sun nuna cewa akwai karuwar firgici da rashin tsari a cikin mayakan saboda ci gaba da ruwan bama-bamai da ke hana su walwala da samun wuraren fakewa masu aminci.
The Nation ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Rundunar sojin saman Najeriya tare da dakarun Operation Hadin Kai da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da dagewa wajen matsa lamba ba tare da sassautawa ba kan kungiyoyin ‘yan ta’adda, tare da kara jaddada kudurinta na kare rayukan fararen hula da dawo da zaman lafiya mai dorewa da tsaro a yankin Arewa maso Gabas,”
In ji sanarwar.
'Yan ta'adda sun kori jama'a
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Amnesty International ta yi korafi kan yadda 'yan ta'adda ke fatattakar mutane a gidajen su a jihar Sokoto.
Amnesty ta ce masu garkuwa da mutane da sauran 'yan ta'adda sun hana mutane sakat a kananan hukumomin Sabon Birni da Isa a 'yan kwanakin nan.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kara kaimi wajen yaki da masu tayar da kayar baya da kai hare-jare kan mutane, musamman a kauyuka.
Asali: Legit.ng
