Goron Sallah: Gwamnan Kano Ya Gwangwaje Ma'aikatan Jiharsa da Kyautar Kudi
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da ba ma’aikatan jihar Kano da tallafin kudi domin su samu kari wajen gudanar da shagulgulan Sallah babba
- Tallafin zai shafi ma’aikatan gwamnati daga mataki na 01 zuwa 14 a faɗin jihar ana saura awanni kadan a fara shagulgula na bikin Eid-el-Kabir
- Gwamnatin Kano ta ce an ɗauki matakin ne domin rage wa ma’aikata nauyin halin ƙunci na tattalin arziki da ake ciki kafin Babbar Sallah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da bayar da tallafin Babbar Sallah na N20,000 ga ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar da kuma ƙananan hukumomi 44.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ba da hutun babbar Sallah, ta aika sako ga musulmin Najeriya
An sanar da hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Musa Tanko-Muhammad, ya fitar a ranar Talata, 26 ga watan Mayu, 2026 a Kano.

Source: Facebook
Jaridar Punch ya ruwaito cewa sanarwar ta bayyana cewa an samar da tallafin ne domin taimaka wa ma’aikata kafin gudanar da bukukuwan Eid-el-Kabir, musamman duba da halin matsin tattalin arziƙin da ake ciki.
Gwamna ya taimaka wa ma'aikatan Kano
A ruwayar The Sun Nigeria, gwamnati ta ce tallafin zai shafi ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati na jihar Kano da kuma ma’aikatan ƙananan hukumomi masu matakin aiki daga mataki na daya zuwa na 14.
Matakin ya zo ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin jihar ta biya albashin watan Mayu, 2026 ga ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi.

Source: Facebook
Sanarwar ta ambato Gwamna Abba Yusuf yana cewa wannan shiri na nuna irin ƙudirin gwamnatinsa wajen kula da jin daɗi da walwalar ma’aikata, waɗanda ya bayyana a matsayin ginshiƙin aikin gwamnati a jihar Kano.
Gwamnan ya ce an ɗauki wannan mataki ne saboda yanayin tsadar rayuwa da kuma ƙarin buƙatun kuɗi da ake fuskanta a lokutan bukukuwa irin na Babbar Sallah.
Abba ya jaddada kudurin gwamnatinsa a Kano
A cewar sanarwar, Gwamnan ya bayyana cewa tallafin zai taimaka wa ma’aikata wajen gudanar da shagulgulan Sallah cikin walwala tare da iyalansu, tare da ƙara masu kwarin gwiwa.
Haka kuma, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da aiwatar da manufofin da suka shafi jin daɗin al’umma da ma’aikata domin inganta aiki da ƙara ƙwazo a aikin gwamnati.
Gwamna Abba ya kuma taya daukacin ma’aikatan jihar da al’ummar Kano murnar zagayowar Eid-el-Kabir, inda ya yi addu’ar samun zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
An yi fashin raguna a Kano
A baya, kun ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun tare dillalan dabbobi daga jihar Kano tare da sace ragunansu da suka tanada saboda shirin babbar Sallah da za a yi a gobe.
Daya daga cikinsu ya ce maharan sun iso da mota, suka harba bindiga sama sannan suka tilasta masu kwanciya kafin satar dabbobin, kana su ka yi awon gaba da su ba tare sun fusknaci turjiya ba.
Lamarin ya sake nuna yadda matsalar tsaro ke barazana ga matafiya da ‘yan kasuwa musamman da ake shirin kasuwar Babbar Sallah a Najeriya, inda masu kasuwancin dabbobi ke cikin fargaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

