Albarkacin Bikin Babbar Sallah, Gwamna Zai Fara Rabon Kayan Abinci ga Ma'aikata
- Gwamnatin jihar Oyo ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen samar da kayan abinci masu rahusa ga ma’aikata kafin Babbar Sallah
- Shinkafa, man girki da raguna na cikin kayayyakin da ake sayar wa ma’aikata cikin rangwame domin rage musu radadin matsin tattalin arziki
- Za a cire kudin kayan daga albashin ma’aikata na tsawon watanni uku daga watan Yulin 2026 zuwa Satumbar shekarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Oyo - Gwamnatin Oyo ta fara rabon kayan abinci masu rangwame ga ma’aikatan gwamnati a fadin jihar domin rage musu wahalar tattalin arziki kafin bikin babbar sallah.
An kaddamar da shirin ne ta hannun Hukumar Bayar da Lamunin Noma ta jihar Oyo (ACCOS) a hedikwatarta da ke Ibadan.

Source: Twitter
Za a raba wa ma'aikata abinci a Oyo
Shugaban hukumar, Sheikh Akeugberu Akeugbagold, wanda ya samu wakilcin shugaban gudanarwa na hukumar, Mista Tunde Oladejo, ya bayyana hakan, in ji rahoton Tribune,
Sheikh Akeugberu Akeugbagold, ya bayyana cewa an kirkiro shirin ne domin tallafa wa ma’aikata su samu damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin sauki.
A cewarsa, gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira miliyan 120 wajen sayo kayayyakin da za a raba wa ma’aikatan.
Ya ce shirin wani bangare ne na manufofin jin dadin ma’aikata na gwamnatin gwamna Seyi Makinde domin inganta rayuwar al’ummar jihar musamman ma’aikatan gwamnati.
Kayayyakin da gwamnati za ta raba
Shugaban hukumar ya bayyana cewa kayayyakin da ake bayarwa cikin rangwame sun hada da buhunan shinkafa, man girkin Kings da kuma ragunan layya.
Ya ce an tsara shirin ne ta yadda ma’aikatan da suka amfana za su biya kudin kayan cikin sauki ta hanyar cire musu daga albashi na tsawon watanni uku.
Akeugberu ya ce za a fara cire kudin kayan daga albashin watan Yulin shekarar 2026, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya kara da cewa wannan mataki yana nuna yadda gwamnatin Makinde ke bai wa walwalar ma’aikata muhimmanci musamman a lokutan bukukuwa.

Source: Original
An bukaci ma’aikata su mara wa gwamnati baya

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci
Hukumar ta kuma bukaci ma’aikatan da suka amfana da shirin su ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar.
Ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi jin dadin jama’a domin amfanin daukacin al’ummar jihar.
Ana sa ran za hau idin babbar sallah a ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2027, yayin da tuni wasu kasashe suka ayyana hutu ga ma'aikata don su yi shagulgulan bikin tare da iyalansu.
An fadi ranar hawan idin babbar Sallah
A wani labari, mun ruwaito cewa, fadar Sarkin Musulmi ta tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah, wanda ke nuna cewa watan Dhul Qa'adah ya kare a ranar Lahadi.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar II ya ayyana Litinin, 18 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, 1447H.
Hakan dai na nufin musulmin Najeriya za su yi hawan idin sallar layya a makon gobe, ranar Laraba, 27 ga watan Mayun, 2026.
Asali: Legit.ng
