Bikin Sallah
Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya bayyana na'ukan dabbobin da ya kamata a yanka a layya, lokacin yanka a layya da yadda za a raba naman layya da sauransu.
Ma'aiatar harkokin cikin gida ta bukaci daukacin musulmin Najeriya su sa kasar a addu'a a wannan lokaci na ibada, tana mai tunatar da su muhimmancin taimakon juna.
Rundunar Operation Hadin Kai da ke aiki a Arewa maso Gabas ta bayyana cewa tana shirye domin magance barazanar Boko Haram a lokacin babbar sallah.
FRSC ta shawarci matafiya su sauya hanyar da suke bi daga Abuja zuwa Kaduna yayin da aka samu cunkoso a tsakanin Nasarawa da Azaga, daga Katari zuwa Jere.
Mazauna Dutse a jihar Jigawa da Funtua, jihar Katsina sun koka kan tashin farashin raguna da sauran dabbobin layya kafin Babbar Sallah, inda rago ya kai N500,000.
Gwamnatin jihar Oyo ta fara rabon kayan abinci masu rangwame ga ma’aikata kafin Babbar Sallah, inda ta kashe sama da Naira miliyan 120 kan shinkafa, mai da raguna.
Sarkin Kano na 15, Aminu Bayero, ya sanar da jami’an tsaro shirinsa na gudanar da Hawan Sallah na 2026 daga fadar Nasarawa a Kano yayin da ake takaddamar masarauta.
Rahotanni daga wasu kasuwannin dabbobi a Kano sun nuna cewa farashin raguna na farawa ne daga N150,000 har zuwa N700,000 ko sama da haka gwargwadon girma.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar II ya bayyana Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, 1447H.
Bikin Sallah
Samu kari