Peter Obi Ya Fadi Yanayin da zai Sa Ya Shiga Daji Ceto Daliban da aka Sace

Peter Obi Ya Fadi Yanayin da zai Sa Ya Shiga Daji Ceto Daliban da aka Sace

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce da shi ne shugaban kasa da kansa zai shiga dajin da aka boye dalibai da malamai da aka sace a Oyo
  • Obi ya ce ba zai jira sama da kwanaki 50 ba kafin daukar mataki, yana mai jaddada cewa jagoranci mai nagarta ne mabuɗin magance matsalar tsaro
  • Ya kuma soki Shugaba Bola Tinubu kan rashin kiran gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a tsawon lokacin da aka shafe ana tsare da wadanda aka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya ce da shi ne shugaban Najeriya, da kansa zai shiga dajin da aka tsare dalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Obi ya ce ba zai bari kwanaki masu yawa su shude ba kafin daukar mataki, yana mai cewa shugabanci nagari shi ne ginshikin magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Dan takarar shugaban kasa, Peter Obi
Peter Obi da zai yi wa NDC takarar shugaban kasa a 2027. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Afia TV a ranar Alhamis.

Magana kan daliban Oyo

A ranar 15 ga watan Mayu ne wasu 'yan bindiga suka kai hari kan makarantu uku da ke karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo.

Rahotanni sun nuna cewa mutum biyu sun rasa rayukansu yayin harin, yayin da akalla dalibai da malamai 45 aka yi garkuwa da su.

Obi ya ce da hakan ta faru a lokacin mulkinsa, da ya isa wurin cikin kwanaki biyu domin tabbatar da an kubutar da duk wadanda aka sace.

Ya ce:

"Shin wannan dajin ba ya cikin Najeriya ne? Zan je cikin kwanaki biyu. Kowa da ke cikin wannan dajin zai fito. Ko da za a samu asarar rayuka, dole ne a fito da kowa."

Obi ya soki Bola Tinubu

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya kuma soki Shugaba Bola Tinubu saboda, a cewarsa, bai kira gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ba a tsawon sama da kwanaki 50 da aka shafe ana tsare da dalibai da malamai.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi yadda za a hana gwamnoni amfani da 'yan sanda jihohi ba bisa ka'ida ba

Ya ce idan aka kama masu laifi, ya kamata a fito da su fili domin jama'a su ga abin da aka cimma, maimakon a rika boye komai.

Obi ya ce:

"A Najeriya komai ana lullube shi. Idan kasashen waje sun kashe ko sun kama masu laifi, suna nuna wa duniya abin da suka yi. Amma a Najeriya komai a boye ya ke ne."
Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso
Dan takarar NDC, Peter Obi tare da mataimakin shi, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi
Source: Facebook

Kiran ADC ga Tinubu kan tsaro

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar ADC ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya mayar da dabarar da aka yi amfani da ita wajen ceto dalibai da malamai da aka sace a Oriire ta zama tsari na kasa.

Jam'iyyar ta ce idan gwamnati ta samu nasarar kubutar da mutanen Oriire, ya kamata a yi amfani da irin wannan dabara wajen ceto sauran mutanen da aka sace a jihohin Kwara, Borno da sauran sassan Najeriya.

ADC ta bayyana cewa dukkan 'yan Najeriya da ke hannun masu garkuwa da mutane sun cancanci gwamnati ta nuna musu irin kulawa da jajircewar da ta nuna a lamarin Oriire.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng