
Satar Shanu







An yi umarni a ga bayan masu tada kayar baya. Ministan harkokin gida yace an ba jami’an tsaro wa’adin nan da Disamba a ga karshen ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Kazeem Bamidele ‘dan shekara 50 a Duniya, yana kotu ana shari’a da shi tare da wasu mutanen da sun tsere, ana tuhumarsu da satar wayoyi 76 a yankin Ajegule.

Ahmed Idris yana neman yin sulhu da EFCC a kotu a shari'ar satar kudi. Lauyan da ya kai kara, Rotimi Jacobs esq ya fadawa Alkali wannan a ranar Larabar nan.

'Yan bindiga sun kai farmaki wurin kiwon shanu wanda ba shi da nisa da filin jirgin saman Sultan Abubakar na jihar Sakkwoto. Sun kwashe sama da shanu 200 .

Dakarun sojin saman Najeriya sun budewa tawaga biyu ta masu satar shanu yayin da suka kai wani samame a Jihar Zamfara da Neja wuta ta jiragen yakin sojojin.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata mota makare da shanu akan titin Ezinifitte/Uga a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabas.
Satar Shanu
Samu kari