2027: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Magana game da Neman Kujerar Abba

2027: Tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Ya Yi Magana game da Neman Kujerar Abba

  • Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi magana kan sabanin da ya shiga tsakaninsa da gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Ya soki manufar “Kano First” tare da cewa tsaro ya kara tabarbarewa a jihar Kano, inda ya bayyana cewa an dauke tsarin 'yan mulkin mallaka
  • Aminu Abdulsalam ya bayyana matsayarsa game da neman kujerar tsohon mai gidansa a jam'iyyar NDC yayin da ke fitar da 'yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi magana game da rikicin da ya raba shi da gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya bayyana cewa an dauki lokaci mai tsawo ana samun takun saka a tsakaninsa da gwamnan, amma babu wanda ya ji bangarensa.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: Yadda Abba Kabir Yusuf ya sasanta manyan 'yan APC a Kano

Aminu AbdulSalam ya ce sun dade suna samun sabani da Gwamna
Tsohon mataimakin gwamnan Kano, Aminu AbdulSalam Gwarzo Hoto: Comrade Aminu AbdulSalam Gwarzo
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, ya soki manufar “Kano First” da gwamna Abba Kabir Yusuf ya bullo da ita bayan sauya shekarsa zuwa jam’iyyar APC.

Tsohon gwamna ya magantu kan manufar Abba

A yayin hirar, Kwamared Aminu Abdulsalam ya ce gwamnatin Kano ta yi kuskure wajen daukar abin da ya kira ra’ayin ‘yan mulkin mallaka da sunan “Kano First.”

A cewarsa:

“Shi gwamna da kansa ya sanya takalmansa ya fita, ra’ayinsa ke nan, hukuncinsa ke nan. Mu hukuncinmu shi ne ba za mu fita ba, muna nan.”

Ya kara da cewa bai amince da ko daya daga cikin dalilan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar na raba hanya da su ba.

Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya ce:

“Duk dalilan da gwamna ya fada, ko daya ban yarda da shi ba, kuma shi ma da ya saurare ni da ba zai yi haka ba.”

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi hasashe da ya ga yawan mutanen da suka fito zaben Tinubu

Kano: Aminu AbdulSalam ya magantu kan takara

Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana cewa sauya shekar Abba Kabir Yusuf ba ta haifar da wani abin a zo a gani ba, domin a cewarsa tsaro ya tabarbare a jihar Kano.

Ya ce:

“Idan ka zo ka yi maganar Kano First, take ce ta ‘yan mulkin mallaka, take ce ta izgili.”

Ya ci gaba da cewa:

“Tun da aka fara Kano First, tsaron Kano ya tabarbare fiye da kowane lokaci a tarihin nan kusa. A Tsanyawa, abubuwan da suka rika faruwa, da kuma a Shanono, haka kuma abubuwan da suke faruwa yanzu a karamar hukumar Gwarzo, an zo daya biyu uku, an kwashe dukiyoyin mutane, an kuma kwashe wasu mutane. Har yanzu akwai mutanen da suke tsare.”

Dangane da siyasar 2027, Aminu Abdulsalam ya bayyana mubaya’arsa ga jam’iyyar NDC, inda ya ce zai goyi bayan duk wanda jam’iyyar ta tsayar takara a zaben gwamna mai zuwa.

Ya kara da cewa tafiyar Kwankwasiyya na da tsarin sulhu da fahimtar juna idan lokaci ya yi. A cewarsa, mulki daga Allah yake, kuma Yana bayar da shi ga wanda Ya so a lokacin da Ya ga dama.a yan mulkin ma

Kara karanta wannan

"Ba a taba maganar sauya sheka tsakanin Kwankwaso da APC ba": Kwankwasiyya

Kano: NDC ta fitar da 'dan takarar Sanata

A baya, kun ji cewa tsohon Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Gaya, ya rasa tikitin takarar Sanata a NDC bayan zaman da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya jaoranta a gidansa da ke Miller 'road' a Kano.

NDC ta tsayar da Kassim Batayya a matsayin ɗan takararta tilo da zai goga da sauran jam'iyyu a fafatawar da za a yi a babban zaben 2027 tare da bayyana kwarin gwiwar zai kai bantensa.

Matakin na zuwa a yayin da NDC ta fara gangamin shiga babban zaben 2027 da ke tafe, inda za a fafata a tsakanin jam'iyyun Najeriya, kuma ana sa ran ci gaba da fitar da 'yan takara a matakai daban-daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng