Yadda Malaman Addinin Kirista Suka kai Ruwa Rana da Tinubu a Aso Villa

Yadda Malaman Addinin Kirista Suka kai Ruwa Rana da Tinubu a Aso Villa

  • Babban limamin cocin Katolika, John Cardinal Onaiyekan, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayyana karara cewa bai yarda da korafe-korafen da bishops suka gabatar ba
  • Onaiyekan ya ce sun yi wa shugaban kasa bayani kan matsalolin tattalin arziki, tsaro da siyasar Najeriya, amma Tinubu ya ce abubuwa na tafiya yadda ya kamata
  • Ya kuma jaddada cewa su ba sa neman mukamin siyasa, sai dai suna sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na fadin gaskiyar halin da 'yan Najeriya ke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Shugaban Cocin Katolika a Abuja, John Cardinal Onaiyekan, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da su karara cewa bai amince da yadda suka bayyana halin da Najeriya ke ciki ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi yanayin da zai sa ya shiga daji ceto daliban da aka sace

Onaiyekan ya ce hakan ya faru ne a lokacin ganawar da shugaban kasa ya yi da mambobin Kungiyar Bishops na Cocin Katolika ta Najeriya (CBCN) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da fastoci
Lokacin da bishop bishop suka gana da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Arise News ta rahoto cewa Onaiyekan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a ranar Juma'a, inda ya yi karin haske kan abin da ya faru a taron.

Martanin Tinubu ba fastoci

Onaiyekan ya ce sun sanar da shugaban kasa cewa tattalin arziki, matsalar tsaro da yanayin siyasar kasar na jefa 'yan Najeriya cikin wahala.

Sai dai ya ce Shugaba Tinubu ya mayar da martani da cewa kasar ba ta cikin halin da suka bayyana.

Punch ta rahoto ya ce:

"Mun gaya masa cewa tattalin arziki ba ya taimakon talakawa, amma ya ce tattalin arzikin yana tafiya daidai. A gaskiya ya bayyana mana karara cewa bai yarda da abin da muka fada ba."

Ya kara da cewa ba su yi mamakin hakan ba domin tun farko ba su sa ran shugaban kasar zai amince da duk abin da suka gabatar masa ba.

Dalilin kiran fastoci ga Tinubu

Kara karanta wannan

Peter Obi ya dura kan Tinubu bayan ya yi kalamai kan yunwa a Najeriya

Onaiyekan ya ce bayanin da shugaban kungiyarsu ya karanta ba ra'ayin mutum daya ba ne, domin an tsara shi ne bayan tuntuba mai zurfi da daukacin kungiyar.

Ya ce an rubuta bayanin sau da dama tare da yin gyare-gyare kafin a gabatar da shi ga shugaban kasa.

Babban limamin ya kuma jaddada cewa ba su da burin karbe mulkin Tinubu ko shiga siyasa, sai dai suna da alhakin fadakar da shugabanni kan hakikanin halin da jama'a ke ciki.

Ya ce sun lura cewa mutane da dama na zagaye da shugaban kasa suna ba shi rahotannin da ke nuna komai na tafiya lafiya, alhali hakan ba shi ne gaskiyar halin da ake ciki ba.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Bola Tinubu da mataimakinsa a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce wannan ne ya sa suka ga wajibi su gabatar masa da hakikanin abin da 'yan Najeriya ke fuskanta, ko da kuwa hakan ba zai yi masa dadi ba.

Obi ya caccaki Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), Peter Obi, ya ce da shi ne shugaban kasa, da kansa zai shiga dajin da aka tsare dalibai da malamai da aka sace a jihar Oyo.

Kara karanta wannan

Sabuwar wakar da Rarara ya fitar kan Isa Pantami ta tayar da kura a Arewa

Obi ya ce ba zai jira sama da kwanaki 50 kafin daukar mataki ba, yana mai cewa shugabanci nagari shi ne mafita ga matsalar rashin tsaro.

Har ila yau, ya soki Shugaba Bola Tinubu kan rashin kiran gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a lokacin da aka shafe ana tsare da wadanda aka sace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng