Farashin Kosasshen Rago Ya Haura N700,000 ana Shirin Babbar Sallah a Jihar Kano
- Yan kasuwar dabbobi sun nuna damuwa kan karancin cinikin raguna yayin da babbar Sallah ke kara gabatowa a jihar Kano
- Bincike ya nuna cewa a wasu kasuwannin dabbobi a Kano, ana sayar da kanana, matsakaita da manyan raguna tsakanin N150,000-N700,000
- Shugaban ƙungiyar dillalan dabbobi ta jihar Kano, Bashir Sule-Dantsoho, ya koka kan karancin ciniki duk da yawan ragunan da aka kawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Masu sayar da raguna a kasuwannin dabbobi na Jihar Kano sun bayyana damuwa kan ƙarancin ciniki duk da cewa farashin raguna ya kai tsakanin N150,000 zuwa N700,000.
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda gabanin fara bukukuwan Eid-el-Kabir, da aka fi sani da sallar layya ko babbar Sallah, ibadar da ta samo asali daga tarihin Annabi Ibrahim (AS).

Source: Facebook
Daily Trust ta ce ana gudanar da wannan ibada ne a ranar 10 ga watan Zul Hijjah, wata na 12 a kalandar Musulunci, ga Musulman da ba su je aikin Hajji ba.
Farashin raguna a jihar Kano
Wani bincike da aka gudanar a kasuwannin dabbobi na Goron Dutse da Kofar Na’isa a cikin birnin Kano ya nuna cewa ‘yan kasuwa sun tanadi dabbobi masu yawa saboda gabatowar babbar Sallah.
A kasuwar Goron Dutse, shugaban ƙungiyar dillalan dabbobi ta jihar Kano, Bashir Sule-Dantsoho, ya ce duk da yawan dabbobin da ake da su, har yanzu babu ciniki sosai saboda matsin tattalin arziki.
Ya ce ƙananan raguna yanzu ana sayar da su tsakanin N150,000 zuwa N200,000, matsakaita kuma tsakanin N350,000 zuwa N500,000, yayin da manyan raguna ke kaiwa N700,000 ko fiye da haka.
A cewarsa, farashin raƙuma yanzu ya kai daga N500,000 zuwa Naira miliyan 3, yayin da bijimai da shanu ke tsakanin N600,000 zuwa Naira miliyan 3 gwargwadon girma da inganci.
Dalilin tashin farashin dabbobi a Kano
Sule-Dantsoho ya bayyana cewa tashin farashin ya samo asali ne daga tsadar abincin dabbobi da kuma kuɗin sufuri daga wuraren kiwo na ciki da wajen jihar.
Ya ce:
“Bara buhun abincin dabbobi ana sayar da shi tsakanin N10,000 zuwa N13,000, amma yanzu ya kai kusan N25,000.

Source: Original
Yan kasuwa sun ce ba a cinikin raguna
Haka kuma a kasuwar Kofar Na’isa, wani dillalin dabbobi mai suna Kabiru Mustapha ya danganta ƙarancin masu saye da halin ƙuncin rayuwa da ake ciki a ƙasar.
Ya ce farashin raƙuma a kasuwar yana tsakanin N500,000 zuwa Naira miliyan 2.5, yayin da shanu ke tsakanin N400,000 zuwa Naira miliyan 3.
A cewarsa, ƙananan raguna suna farawa daga N150,000, yayin da matsakaita da manya ke kaiwa sama da N550,000, kamar yadda The Nation ta kawo.
Ya ƙara da cewa mutane da dama sun fi son jiran kwanaki kaɗan kafin sallah ko ma ranar sallah domin ganin ko farashin zai sauka.
Raguna aun yi tsada a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa farashin raguna ya yi tashin gwauron zabi a wsu kasuwannin jihar Kaduna yayin da musulmi ke shirye-shiryen sallar layya.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya sa mutane da dama sun dakatar da sayen dabbar da za su yi layya da ita duk da wadatar dabbobin a kasuwanni.
Wani dillalin dabbobi a kasuwar Rigasa, Alhaji Suleiman Adamu, ya danganta tashin farashin da tsadar sufuri, abincin dabbobi da kuma matsalar tsaro
Asali: Legit.ng


