Sojoji Sun Cafke Yaro 'Dan Shekara 15 da Zargin Ayyukan Ta'addanci

Sojoji Sun Cafke Yaro 'Dan Shekara 15 da Zargin Ayyukan Ta'addanci

  • Dakarun rundunar operation hadin kai sun cafke wani matashi da ake zargin ɗan ta’adda ne a garin Gubio na jihar Borno da ke Arewa maso Gabas
  • An kama matashin mai shekara 15 ne yayin wani samame da aka gudanar tare da haɗin gwiwar CJTF a yakin da jami'an tsaro ke yi da ta'addanci
  • Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya amsa cewa yana cikin wata ƙungiya da ke kai hare-hare kan matafiya a yankin Kareto tare da hallaka bayin Allah

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Dakarun Bataliya ta 149 ƙarƙashin rundunar 'operation' hadin kai tare da haɗin gwiwar rundunar sa-kai ta CJTF sun kama wani matashi da ake zargin yana da hannu a ayyukan ta’addanci a garin Gubio da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Baki ya yanka wuya, kotu ta ingiza keyar kakakin PDP zuwa kurkuku kan taba gwamna

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da kamen ne a ranar 14 ga watan Mayu, 2026 da 1.20 na rana yayin wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai domin bibiyar waɗanda ake zargi da ayyukan tada ƙayar baya a yankin.

An kama yaro a cikin yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno, jihar da ke fama da rashin tsaro Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafin X ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2026.

Sojoji sun kama matashin dan ta'adda

Jaridar Daily post ta wallafa cewa cewar bayanin Zagazola, an gano wanda ake zargin da suna Umar Zacharria mai shekara 15, ɗan ƙaramar hukumar Jere ta jihar Borno.

Majiyoyin tsaro da aka ambata a rahoton sun ce matashin ya amsa cewa yana cikin wata ƙungiya da ake zargi da kai hare-hare kan direbobi da matafiya a yankin Kareto.Jami’an tsaro sun fara bincike kan wanda ake zargin

Rahoton ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike mai zurfi domin gano irin rawar da matashin ya taka a ayyukan ƙungiyar tare da gano alaƙarsa da sauran waɗanda ake zargi.

An kama matashin yayin wani samame a Borno
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno Hoto: The Governor of Borno State
Source: Twitter

Majiyoyin sun ce:

“A halin yanzu matashin yana tsare a hannun sojoji, inda ake ci gaba da bincike domin gano girman hannunsa a lamarin da kuma yiwuwar alaƙarsa da sauran 'yan kungiyar ta'addancin."

Kara karanta wannan

Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River

Sojoji na ci gaba da yaki da yan ta'adda

A cikin ‘yan shekarun nan, jami’an tsaro a arewa maso gabashin Najeriya sun ƙara kaimi wajen gudanar da samame da sintiri domin dakile hare-haren masu tayar da ƙayar baya.

Sun zage damtse wajen wannan aiki musamman a wasu yankunan jihar Borno da ke fama da matsalar tsaro da ta shafe shekaru ana fafata wa da ita.

'operation' hadin kai na daga cikin manyan ayyukan soji da gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar domin yaƙi da ƙungiyoyin ‘yan tada ƙayar baya a yankin Arewa maso Gabas.

Sai dai hukumomi ba su fitar da ƙarin bayani ba kan ko akwai wasu karin mutane da aka kama a yayin samamen da aka gudanar a Gubio.

Sojoji sun hallaka fararen hula

A wani labarin, kun ji cewa ana ci gaba da magana kan harin sojojin saman Najeriya wanda ake zargin ya hallaka fararen hula da dama a jihar Zamfara a yakin da ake yi da yan ta'adda ke kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Shugabar ALGON a Kano ta sha da kyar bayan 'yan daba sun far mata

Majiyoyi daga yankin sun ce kasuwar da aka kai harin, wuri ne wanda yake hada farar hula da 'yan ta'adda kuma mafi yawan kauyukan da ke Arewacin garin Zurmi suna rayuwa ne a karkashin ikon 'yan ta'addan.

Babu wanda ya iya tantance adadin waɗanda aka kashe ko suka ji rauni yayin harin saman, amma sun haɗa da ’yan ta’adda da kuma farar hula mazauna yankin da ake ganin ya yi kaurin suna a harkar ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng