Mutane 9 da Aka Sace Sun Taki Sa'a, Sun Shammaci 'Yan Bindiga a Jihar Katsina

Mutane 9 da Aka Sace Sun Taki Sa'a, Sun Shammaci 'Yan Bindiga a Jihar Katsina

  • Dakarun rundunar sojojin Operation Fansan Yamma sun ceto mutum tara da suka tsere daga hannun masu garkuwa a Katsina
  • Sojojin sun kuma kwato shanu hudu da tumaki 52 da 'yan ta'adda suka sace kuma sun kuma kama wani da ake zargi da alaka da ayyukan ta'addanci
  • Rundunar sojojin ta ce za ta ci gaba da matsa wa miyagu lamba har sai an kawo karshen ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa da ke aiki Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun ceto mutum tara da suka tsere daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina.

Gwarzan sojojin sun kwato dabbobi 56 da aka sace tare da kama wani da ake zargi da alaka da 'yan ta'adda a wasu hare-hare daban-daban da suka gudanar a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani mutumi da ake zargi da ƙulla kasuwanci da yan bindiga a Katsina

Sojoji.
Dakarun runamdunar sojojin Najeriya da ke yaki da matsalar tsaro Hoto: Nigerian Army
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa jami'in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.

Mutum 9 sun shammaci yan bindiga a Katsina

A cewarsa, dakarun sojoji na sashe na 2 sun ceto mutanen yayin da suke sintiri a yankin karamar hukumar Faskari da ke Kudancin Katsina

Ya ce mutanen da aka ceto sun hada da mata uku, maza hudu da yara biyu.

Aliyu Danja ya bayyana cewa an yi garkuwa da su ne a ranar 9 ga Yulin 2026 a kan hanyar Tsafe zuwa Kuchere da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Binciken farko ya nuna cewa mutanen sun samu damar tserewa ne bayan masu garkuwar sun yi barci, kafin dakarun suka same su a cikin daji tare da ceto su.

Ya ce:

"A halin yanzu wadanda aka ceto suna hannun jami'an tsaro, inda ake kammala wasu matakai kafin a mika su ga iyalansu."

Kara karanta wannan

An yi kicibis, sojoji sun yi ram da 'dan bindiga a hanyar sintiri

Sojoji sun kwato dabbobi 56

A wani samame na daban, Kanal Danja ya ce dakarun sojojin sun kai dauki bayan samun sahihan bayanan sirri cewa 'yan ta'adda na kokarin sace dabbobi a karamar hukumar Bakori.

Ya ce 'yan ta'addan sun bude wa sojoji wuta, amma sun tsere zuwa cikin daji bayan dakarun sun yi galaba a kansu, kamar yadda Leadership ta kawo.

Sojojin sun kwato dabbobi 56 da suka hada da shanu hudu da tumaki 52, wadanda ake tsare da su kafin a mika su ga hukumomin da suka dace.

Katsina.
Taswirar jihar Katsina d ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kama wanda ake zargi da ta'addanci

Haka kuma, dakarun sun cafke wani da ake zargi da alaka da ayyukan ta'addanci yayin sintiri a karamar hukumar Danmusa.

A cewar Aliyu Danja, kayayyakin da aka samu tare da wanda ake zargin sun nuna cewa yana iya kasancewa yana da alaka da ayyukan 'yan ta'adda, amma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansa.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ƴan sanda sun cafke mayakan Lakurawa da ke addabar garuruwan Arewa

Sojoji sun ragargaji yan bindiga a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojoji ta Operation Fansan Yamma sun dakile hare-haren 'yan bindiga a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara.

Sojojin sun kashe wani fitaccen kwamandan 'yan bindiga tare da tarwatsa wani shirin kai babban hari ta hanyar luguden wuta daga sama.

Bugu da kari, rundunar sojin sama ta Operation Fansan Yamma kai farmaki kan 'yan bindiga kusan 300 da ke kan babura, inda suka kashe da dama daga cikinsu a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262