Bikin Sallah: Gwamna Zulum Ya Raba Shinkafa Mai Dauke da Hoton Tinubu
- Gwamna Babagana Umara Zulum ya kaddamar da raba tallafin abinci ga marasa karfi a karkashin shirin Renewed Hope a fadin jihar Borno
- Legit Hausa ta gano cewa an kaddamar da rabon abincin ne a birnin Maiduguri, inda aka tara jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki
- Gwamnatin Zulum ta bayyana cewa shirin tallafin zai shafi mata, marayu, ‘yan gudun hijira da sauran marasa karfi a fadin jihar da kewaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da raba tallafin sallah da aka tsara a karkashin shirin Renewed Hope ga marasa karfi a fadin jihar.
An fara raba kayayyakin ne a dakin taro na Prime Lodge da ke birnin Maiduguri, inda aka fara rabon a gaban jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki a harkar jin kai.

Source: Facebook
Mai magana da yawun gwamna Zulum, Dauda Iliya ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa jama'ar da suka samu tallafin za su amfana lura da lokacin bikin sallar layya ya karato.
Babagana Zulum ya raba shinkafar Bola Tinubu
A jawabinsa yayin raba tallafin, Gwamna Zulum ya yi godiya ga matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa tallafin abinci da ta kawo wa marasa galihu.
Gwamnan ya ce shirin zai taimaka wajen tallafa wa mata zawarawa, marayu, ‘yan gudun hijira da sauran masu bukata ta musamman a jihar.
Ya ce suna matukar jin dadin irin wannan hadin kai da ke tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Borno wajen inganta rayuwar jama’a da rage radadin talauci.
Zulum ya kuma jaddada cewa duk da kalubalen tsaro da jihar ta fuskanta tsawon shekaru, al’ummar Borno sun ci gaba da nuna hakuri, jarumta da juriya.
Bayani kan raba tallafin abincin
Gwamnan ya bayyana cewa rabon kayan tallafin wani bangare ne na manyan shirye-shiryen jin kai da gwamnati ke aiwatarwa domin rage matsin rayuwa a cikin al’umma.
Zulum ya bukaci kwamitin rabon tallafin da su tabbatar sun yi gaskiya, adalci da rikon amana wajen aiwatar da aikin, domin tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai suka amfana.

Source: Facebook
A nasa bangaren, shugaban kwamitin rabon tallafin, Dr Abba Bashir Dankellori, ya nuna godiya ga matatar shugaban kasa bisa tallafi, yana mai cewa zai taimaka wa iyalai da dama domin su gudanar da sallah cikin walwala.
Ya kuma yabawa Gwamna Zulum bisa jagoranci mai cike da sadaukarwa da kishin al’umma, yana mai cewa irin wannan aiki na jin kai na kara karfafa zaman lafiya da hadin kai.
Sojoji sun yi shirin babbar sallah
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun ce Boko Haram sun yi shirin kai hari a lokacin babbar sallah a Arewa maso Gabas.
Sai dai sojojin Najeriya sun sanar da cewa sun riga sun dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa 'yan ta'addan ba su yi nasara ba.
Rundunar Operation Hadin Kai ta yi kira ga al'umma da su bi matakan tsaron da ta fada domin ganin sun yi bikin sallah lami lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

