Karatun Ilimi
Ɗaliban kwalejin aikin janta a Taraba sun gudanar da zanga-zanga bayan 'yan daba sun shiga ɗakin kwanansu, suka ci zarafin daliba da yanke mata yatsa.
Gwamnati ta jaddada matsaiyarta na riƙe makarantun sakandare, inda ta kawar da fargabar sayar da su sakamakon takaddamar da ta ɓulla a King's College da ke Lagos.
Gwamnatin tarayya ta ce ɗaliban Najeriya za su fara samun 100MB na data kyauta kowace rana daga 1 ga watan Oktoba 2026 domin karatun zamani a saukake.
Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya ce za a kama yaran da suka kai zuwa makaranta da aka samu kan tituna lokacin karatu domin inganta ilimi a jihar.
Kungiyar dalibai ta ce manufofin Tinubu na inganta rayuwar ɗalibai, yayin da ƙungiyar ta bayyana shirin tattara kuri’u miliyan 10 domin mara wa shugaban baya a 2027.
Wani yaro mai shekaru 11 da ke makarantar firamare a Afirka ta Kudu ya zargi ɗalibai huɗu da tilasta masa kaciya a makaranta, lamarin da ’yan sanda ke bincike.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin sake gyara tsarin Asusun Bayar da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) tare da yafe basussuka.
Matar tsohon Kwamishinan Ilimi na Niger da ’ya’yanta uku sun mutu a hatsarin mota, yayin da ’yarta daya ta tsira da munanan raunuka da ake fargabar rayuwarta.
Kungiyar BBYDI ta fara horar da matan Kaduna 20 a fannin fasahar AI da kimiyyar bayanai. Shirin na tsawon wata shida ne da tallafin kasar Kanada don bunkasa ilimi.
Karatun Ilimi
Samu kari