Hukunce Hukuncen Dabbobin da Ya Kamata a Yanka domin Layya

Hukunce Hukuncen Dabbobin da Ya Kamata a Yanka domin Layya

Legit Hausa ta haɗa muku rahoto na musamman game da hukunce-hukuncen da suna shafi dabbobin da za a yanka a sallar layya da yadda za a yi amfani da naman.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - A ranar Laraba, 27 ga watan Mayun 2026 za a gudanar da bikin sallar layya a Najeriya da kasashen Musulmi a fadin duniya.

Mutane da dama, musamman mawadata, za su yanka dabbobi daban-daban domin aikata ibadar layya da Musulunci ya shar'anta.

Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri
Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri a hagu da wasu dabbobi a dama. Hoto: Naziru Usman| Livestock Farmer
Source: Facebook

A wannan rahoto, Legit Hausa ta haɗa muku bayani na musamman game da wasu hukunce hukuncen da suka shafi dabbobin da za a yanka a lokacin sallar layya.

Dabbobin da za a yanka a layya

A tattaunawa da malamin Musulunci, Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri, ya bayyana cewa mafi kyawun dabbobin da ya kamata a yanka nau'uka takwas ne.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi barazana ga masu alakanta shi da goyon bayan 'yan bindiga

Ya ce mafi kyawun nau’in dabbobin da za a yi layya da su su ne rago ko tinkiya, akuya ko taure, saniya ko bujumi, raƙumi ko rakuma.

Game da shekarun su, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo ya wallafa a Facebook cewa dole:

1. Rago/tinkiya su kai wata shida

2. Akuya/taure su kai shekara daya

3. Saniya/bijimi su kai shekara biyu

4. Raƙumi/raƙuma su kai shekara biyar

Wasu ragunan layya
Wasu raguna da za a kai kasuwa a Adamawa. Hoto: Livestock Farmer
Source: Facebook

Sheikh Al-Juzuri ya kara da cewa mafi alheri daga cikin dabbobi su ne masu ƙiba, masu nama mai yawa, cikakku ta fuskar halitta kuma masu kyau idan aka kalle su.

Ya ce:

"A cikin Sahihul Bukhari an ruwaito daga Anas ibn Malik (Allah ya yarda da shi) cewa Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) yana yin layya da raguna biyu masu ƙaho, farare masu ɗigon baƙi."

Dabbobin da ya kamata a nisanta a layya

Dangane da dabbobin da bai kamata a yanka su a matsayin layya ba a lokacin babbar sallah, Sheikh Al-Juzuri ya ce su ne:

1. Waɗanda aka yanke musu rabin kunnuwa ko fiye

Kara karanta wannan

"Kada a zalunci El Rufa'i": Tsohon jigon APC ya roki dattawan Arewa su saka baki

2. Waɗanda aka tsaga musu kunnuwa

3. Waɗanda aka huda kunnuwansu

4. Marasa nama ko bargo

5. Waɗanda aka cire musu ƙaho gaba ɗaya

6. Waɗanda suka makance ko da idanunsu suna bude (Ko da ido daya ne)

7. Masu dingishi sauran na'ukan rashin lafiya

Za a soke rakumi a sallar layya
Yadda ake kokarin soke wani rakumi a Masar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma, ya kara da cewa ana saka wasu makamantan su cikin wannan hukunci, don haka ba a son a yanka:

1. Raƙuma, shanu da awaki da aka yanke masu rabin wutsiya ko fiye

2. Dabbar da aka yanke mata azzakari

3. Dabbar da ta rasa wasu hakora, ko na gaba ko na baya

3. Dabbar da aka yanke mata nono

Hukuncin yanka dabbar layya

Malamin ya ce ya halatta ga musulmi ya wakilta wani musulmi ya yanka masa dabbar layya a madadinsa, Sai dai ya ce dole sai bayan yankan liman za a yi yanka.

Sheikh Usamn Al-Juzuri ya kara da cewa malamai sun yi ittifaƙi cewa ya fi alheri mutum ya yanka da kansa, sai dai idan akwai larura.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

An yanka wata dabbar layya
Yadda aka yanka saniya a sallar layya a Pakistan. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun raba naman layya a Musulunci

Sheikh Usman Muhammad Al-Juzuri ya ce an halatta a raba naman layya, a ci, a ba da shi sadaka kuma a yi kyauta da shi.

Malamin ya ce:

"Imam Malik ya ce babu iyaka ga abin da za a ci ko a bayar ko a raba, ko danye ko dafaffe."

Ya kara da cewa wasu malamai sun ce mustahabbi ne a raba shi kashi uku: a ci kashi ɗaya, a bayar da sadaka kashi ɗaya, a ba kyauta kashi ɗaya.

Kasuwar dabbobi a jihar Adamawa
Layin 'yan awaki a kasuwar Jada, jihar Adamawa. Hoto: Livestock Farmer
Source: Facebook

Wasu kuma sun ce za a iya cin rabi, amma shafin Muslim Aid ya ce ya fi dacewa a bayar da wani ɓangare na naman a matsayin sadaka ga wadanda ba su yi layya ba.

Sojoji sun yi shirin sallar layya

A wani labarin, kun ji cewa dakarun Operation Hadin kai da ke Arewa maso Gabas sun bayyana cewa sun yi shirin samar da tsaro a lokacin sallah.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Matasa sun yi bore a Kano, sun kona wani ginin gwamnati

Sun fadi haka ne yayin da suka ce sun samu bayanan tsaro da ke nuna cewa 'yan ta'addan Boko Haram na son amfani da lokacin wajen kai hari.

Rundunar ta yi kira ga shugabannin al'umma da suka hada da sarakuna, kungiyoyi, 'yan jarida da sauransu da su ba jami'a tsaro hadin kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng