Eid El Adha: Sarkin Musulmi Ya Fadi Ranar da Za a Yi Babbar Sallah a Najeriya
- Fadar Sarkin Musulmi ta tabbatar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah, wanda ke nuna cewa watan Dhul Qa'adah ya kare a ranar Lahadi
- Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar II ya ayyana Litinin, 18 ga watan Mayu a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah, 1447H
- Hakan dai na nufin musulmin Najeriya za su yi hawan idin sallar layya a makon gobe, ranar Laraba, 27 ga watan Mayun, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sokoto - Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, 2026 a Najeriya.
Sultan ya bayyana ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, 2026 a matsayin 1 ga watan Dhul Hijjah na shekarar 1447H, watan sallar layya.

Source: Getty Images
An samu labarin ganin wata a Najeriya
Wani dan kwamitin ganin wata na fadar sarkin musulmi kuma masanin ilimin taurari, Simwal Usman Jibrin ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.
Simwal ya ce:
"Assalamu alaikum, Mai Alfarma Sarkin Musulmi na Sakkwato ya bayyana gobe Litinin, 18 ga Mayu, a matsayin ranar farko ta watan Dhul Hijjah.
"Nan ba da jimawa ba fadar sarkin musulmi za ta fitar da cikakken bayani a hukumance in sha Allah."
Hakan dai na nuna cewa al'ummar musulmi a Najeriya za su yi babbar sallah watau 'Eid El Adha' a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 2026, daidai da 10 ga watan Dhul Hijjah, 1447.
Sallah: Sanarwa daga fadar sarkin Musulmi
Jim kadan kuwa, fadar Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwa a hukumance, tana mai tabbatar da ganin jaririn watan Dhul Hijjah a Najeriya, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Sanarwar na ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin kula da harkokin addinai na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu.
Ya ce mai alfarma Sarkin Musulmi wanda shi ne shugaban Majalisar ƙoli mai kula da harkokin musulunci a Najeriya (NSCIA), Alhaji Sa'ad Abubakar ya ayyana Litinin a matsayin 1 ga Dhul Hijjah.

Source: Facebook
Farfesa Sambo Wali ya ce:
"Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni, shugaban Majalisar kula da harkokin musulunci (NSCIA) ya bayyana Litinin a matsayin ranar farko a watan Dhul Hijjah.
Wannan wata na Dhul Hijjah na da matuƙar daraja a addinin musulunci, a cikinsa ne musulmi ke yin ibadar aikin hajji, ɗaya daga cikin rukunan addinin.
Farashin dabbobin layya a Katsina
Yayin da ake tunkarar babbar Sallah, Wakilin Legit Hausa ya zanta da Awwal Bala, wani mai sayar da dabbobi don jin yadda farashin dabbobin layya yake a bana.
Awwal Bala ya bayyana cewa:
"Bana an samu karin kudin dabbobi, amma mu a nan abin bai yi muni kamar yadda muke ji a wasu garuruwa ba, domin karin ba mai yawa ba ne.
"Har yanzu, za ka samu rago mai maiko a kan N150,000, sannan rago wanda ya cika sunansa zai kai kamar N250,000 zuwa N300,000, wanda idan a wasu jihohi ne, zai kai N400,000 zuwa N500,000."

Kara karanta wannan
Sarki Aminu Ado Bayero ya shirya hawan Sallah a Kano, ya aika saƙo ga jami'an tsaro
Wani magidanci, Malam Bashir Bagari da muka zanta da shi, ya bayyana cewa saboda tsadar dabbobi a bana da rashin kudi a hannun jama'a, suka hada N600,000 don yin ginsami da saniya.
"Ai malam ina fada maka, yanzu ginsami ne kawai mutum zai shiga ya samu naman da za a ci a gidansa cikin rufin asiri. To raguna ne sun yi kudi, ga kuma mu nan babu kudin."
- Malam Bashir Bagari.
An ga watan sallar layya a Saudiyya
A wani labarin, kun ji cewa hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa an ga jinjirin watan Dhul Hijjah a ranar Talata, 29 ga watan Dhul Qa'adah, 1447 daidai da 17 ga watan Mayu.
A cewar sanarwar da mahukuntan Saudiyya suka fitar, alhazai za su yi hawan Arafah a ranar Talata, 9 ga watan Dhul Hijjah, wanda zai yi daidai da 26 ga watan Yuni, 2026.
Wannan sanarwa dai ta tabbatar da cewa watan Dhul Qa'adah ya kare, yau Litinin ne 1 ga watan Dhul Hijjah, 1447H, sannan ranar Laraba, 27 ga Mayu za a yi sallah.
Asali: Legit.ng

