Alhaji daga Najeriya Ya Rasu a Saudiyya bayan Gama Hawan Arafa
- Wani Alhaji dan Najeriya da aka ce dan asalin jihar Bauchi ne da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 ya rasu a ranar Laraba a Muzdalifah jim kadan bayan isowarsa daga Arafa
- Shaidu sun ce jami’an ‘yan sandan Saudiyya tare da ma’aikatan lafiya na gaggawa ne suka fitar da mamacin a kan keken daukar marasa lafiya jim kadan bayan faruwar lamarin
- Legit Hausa ta bibiyi shafukan sada zumunta na hukumar Al-Hazai ta kasa (NAHCON) domin duba ko ta yi karin haske game da Alhajin da aka sanar da cewa ya rigamu gidan gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudiyya - Wani Alhaji dan Najeriya da ake kyautata zaton dan asalin jihar Bauchi ne da ke gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026, ya rasu a ranar Laraba a Muzdalifah.

Kara karanta wannan
Ranar Sallah: Ƴan sanda, NSCDC, FRSC sun dauki muhimman matakai na samar da tsaro
An ga jami’an tsaron Saudiyya da ma’aikatan lafiya na gaggawa suna kwashe gawar mamacin daga wurin da sanyin safiya bayan mahajjata sun kwana suna tafiya daga Arafa zuwa Muzdalifah.

Source: Getty Images
Yadda aka fitar da gawar Alhajin
Shaidu sun shadawa Daily Trust cewa jami’an ‘yan sandan Saudiyya tare da jami’an ma’aikatan lafiya na gaggawa ne suka fitar da mamacin a kan keken daukar marasa lafiya.
An kuma ga wasu jami’ai biyu da ake kyautata zaton suna cikin tawagar mahajjatan jihar Bauchi suna rakiyar gawar yayin kwashe mamacin.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin da abin ya shafa ba su tabbatar da sunan mamacin a hukumance ba.
Har ila yau, ba a san musabbabin rasuwar ba domin jami’ai ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Lamarin na zuwa ne a wani lokaci mai wahala na aikin Hajji wanda ke tattare da yawan zirga-zirgar mahajjata tsakanin wurare masu tsarki karkashin tsananin yanayin zafi da dumbin jama’a.
Tun da farko dubban mahajjatan Najeriya sun isa Muzdalifah cikin dare bayan hudubar ranar Arafa suna addu’o’i da rokon Allah.

Source: Getty Images
NAHCON ba ta magantu ba
Tun bayan faruwar lamarin, Legit Hausa ta bibiyi shafukan sada zumunta na X da Facebook da hukumar NAHCON ke fitar da sanarwa amma ba ta ce komai ba.
A shafin X, NAHCON ta yi magana kan hawan Arafa da cewa:
“Yayin da mahajjatan Najeriya ke haduwa da miliyoyin Musulmai daga sassa daban-daban na duniya a wannan rana mai alfarma ta Arafa, muna mika sakonnin addu’o’i da gaisuwa ga dukkan mahajjatanmu a wannan lokaci mai muhimmanci ta fuskar addini.
"Ranar Arafa ce kololuwar aikin Hajji, rana ce ta rahama, gafara, addu’a da cikakkiyar mika kai ga Allah Madaukakin Sarki."
Darusan ranar Arafa guda10
A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi nasiha game da ranar Arafa.
Malamin ya jero wasu darusa 10 da ya ce ya kamata kowane Musulmi ya yi aiki da su domin samun lada sosai a ranar Arafa da ke da falala.
Muhimman darusan da malamin ya jero sun hada da hakuri, hadin kai, neman kusanci zuwa ga Allah da ya ce duk ana samun su a ranar Arafa.
Asali: Legit.ng
