Ranar Sallah: Ƴan Sanda, NSCDC, FRSC Sun Dauki Muhimman Matakai na Samar da Tsaro
- Rundunar ‘yan sandan Legas ta baza jami’ai sama da 10,000 zuwa masallatan idi, manyan hanyoyi da wuraren taruwar jama’a domin tabbatar da tsaro yayin bikin Sallah
- Hukumar NSCDC ta tura jami’ai sama da 56,000 tare da motocin sintiri, kwale-kwale da jami’an K-9 domin hana karya doka da kai dauki cikin gaggawa
- Ita ma hukumar FRSC ta sanar da baza jami’ai 30,000 a fadin Najeriya domin rage hadurran hanya da tabbatar da zirga-zirga lafiya a lokacin bukukuwan Sallah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Legas - Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta sanar da tura sama da jami’ai 10,000 zuwa wurare masu muhimmanci domin tabbatar da tsaro yayin bikin babbar Sallah.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Fatai Tijani ne ya bayyana hakan, inda ya ce an dauki matakin ne domin kara sintirin jami’ai, dakile laifuffuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a yayin da ake bikin Sallah.

Source: Twitter
An jibge 'yan sanda a masallatan idi
Ya ce rundunar ta kara kaimi wajen gudanar da samame a yankunan da ake zargin masu aikata laifi na yawaita, lamarin da ya kai ga cafke mutane da dama, in ji rahoton The Nation.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa rundunar ta shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana ta tsaro, musamman a lokacin da ake samun cunkoson jama’a da motoci a Legas saboda bukukuwan Sallah.
A cewarsa, an riga an baza jami’ai zuwa wuraren ibada, manyan hanyoyi da sauran wuraren taruwar jama’a domin tabbatar da zaman lafiya da doka.
Ya ce:
“Idan kuka duba da kyau za ku ga yawaitar jami’an ‘yan sanda a sassa daban daban na jihar.”
Ya kara da cewa an tanadi matakan gaggawa domin hana duk wata matsalar tsaro kafin da bayan bukukuwan Sallah.
NSCDC ta baza jami’ai 56,000
A gefe guda kuma, Jaridar Punch ta ruwaito cewa hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) ta sanar da tura sama da jami’ai 56,000 domin gudanar da aikin tsaro a lokacin bikin.
Babban kwamandan hukumar, Ahmed Audi ya umarci a baza motocin sintiri, motocin daukar marasa lafiya, kwale-kwale da kuma jami’an K-9 domin kai dauki cikin gaggawa idan bukatar hakan ta taso.
Mai magana da yawun NSCDC, Babawale Afolabi ya ce an sanya dukkan rundunonin musamman cikin shirin ko-ta-kwana domin hana karya doka.
Ya ce rundunonin da za su shiga aikin sun hada da Mining Marshals, Special Intelligence Squad, Crack Squad, Female Special Force da Rapid Response Squad.

Source: Twitter
FRSC ta tura jami’ai 30,000
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ita ma ta sanar da baza jami’ai 30,000 da suka hada da Regular da Special Marshals domin tabbatar da tsaron matafiya a lokacin bukukuwan Sallah.
Hukumar ta ce aikin na musamman ya fara ne daga ranar 25 ga watan Mayu kuma zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga watan Mayu, 2026, in ji rahoton Radio Nigeria.
FRSC ta bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce rage hadurran hanya, cunkoson ababen hawa da kuma tabbatar da kai dauki cikin gaggawa yayin yawaitar zirga-zirgar jama’a a lokacin bukukuwan Sallah.
An ba ma'aikata hutun babbar sallah
A wani labari, mun ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta ba da hutun kwanaki biyu ga ma'aikata domin su samu damar gudanar da shagulgulan babbar Sallah ta bana 2026.
Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Oji ya taya daukacin musulmi murnar zagayowar babbar sallah, daya daga cikin ibadun addinin musulunci.
Gwamnatin tarayya ta kuma buƙaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a da nazari domin neman shiriyar Allah ga Najeriya.
Asali: Legit.ng


