Benue: Ƴan Bindiga Sun Yi Yunkurin Kai Hari a Wurin Zaben Fitar da Gwani na APC
- Dakarun Operation Whirl Stroke sun kama wani da ake zargi bayan dakile yunkurin ‘yan bindiga na kawo cikas ga zaben APC a Benue
- Sojojin sun kwato bindigar AK-47, harsasai da motar Sienna da ake zargin maharan sun shirya amfani da ita wajen tserewa bayan harin
- Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kuma cafke wasu da ake zargi da alaka da ‘yan ta’adda a jihohin Kwara da Benue a lokuta daban daban
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Benue - Dakarun Operation Whirl Stroke sun dakile wani yunkuri da wasu ‘yan bindiga suka yi na kawo cikas ga zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Benue.
Rahoton ya nuna cewa lamarin ya faru ne ranar 16 ga Mayu, 2026, a garin Aliade da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas a jihar Benue.

Source: Original
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Benue
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya fitar ranar Juma’a, in ji rahoton Punch.
Manjo Janar Michael Onoja ya bayyana cewa sojojin sun yi gaggawar daukar mataki bayan samun bayanan sirri kan yunkurin wasu 'yan ta'adda dauke da makamai na kai hari.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi artabu da ‘yan bindigar da ake zargin sun shirya tayar da rikici yayin zaben fitar da gwani na APC.
“A jihar Benue, ranar 16 ga Mayu, 2026, sojoji a Aliade da ke Gwer ta Gabas sun dakile wani yunkuri na wasu ‘yan bindiga da suka so tada rikici a zaben fitar da gwani na APC,” in ji sanarwar.
Nasarar da sojoji suka samu a harin
A yayin aikin, an kama mutum guda da ake zargi yayin da sauran suka tsere. Sojojin sun kuma kwato wata motar Toyota Sienna da ake zargin maharan suka tanada domin guduwa bayan kai harin.
Haka zalika, an kwato bindiga kirar AK-47, gidajen harsasai da su kansu alburusan masu yawa daga hannun wadanda ake zargin.
Maj. Gen. Onoja ya kuma bayyana cewa dakarun Operation Savannah Shield sun kai farmaki kan wasu hanyoyin sadarwa da ake amfani da su wajen taimaka wa ‘yan ta’adda da makamai da magunguna a jihar Kwara.

Source: Twitter
An kama shugaban kungiyar 'yan ta'adda
Sanarwar ta kara da cewa sojoji da ke aiki a Bokungi da ke karamar hukumar Edu sun kama wani babban shugaban kungiyar 'yan ta'adda yayin da yake tafiya zuwa Ilorin daga yankin Ndeji.
An ce wayoyin salular wanda ake zargin sun kunshi hotuna da bidiyo da ke nuna shi dauke da manyan bindigogi da kuma dumbin kudaden da ake zargin an karbe su ta hanyar karbar haraji ko kwace daga jama’a.
Hakazalika, ranar 16 ga Mayu, sojoji sun gudanar da aikin bincike a Tunga Maje da ke karamar hukumar Kaiama inda suka kama wani da ake zargi da bai wa ‘yan ta’adda bayanai.
'Yan bindiga sun bude wa sojoji wuta

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun far wa mutane bayan sun dawo daga sayayyar kayan Sallah a Katsina
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kashe mutane huɗu, ciki har da sojoji biyu, a harin da suka kai Ijaha Ikobi, Benue.
An ce 'yan bindigar sun yi wa sojojin kwanton bauna a lokacin da suka kai dauki garin, kuma ana zargin sun kwace makamansu.
Shugaban ƙaramar hukumar Apa ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fitar da gawarwakin sojojin da aka kashe daga yankin.
Asali: Legit.ng

